Sojoji Sun Karbi Mulki yayin da Zanga Zanga Ta Tsananta a Bangladesh, An Samu Bayanai

Sojoji Sun Karbi Mulki yayin da Zanga Zanga Ta Tsananta a Bangladesh, An Samu Bayanai

  • Mulkin firaministar Bangladesh, Sheikh Hasina na shekaru 15 ya zo karshe a ranar Litinin 5 ga Agusta bayan ta yi rubuta takardar murabus
  • Murabus din Sheikh Hasina na zuwa ne bayan shefe watanni ana zanga-zangar adawa da matakin gwamnatinta na rusa guraben ayyuka
  • A halin yanzu, sojoji sun karbi mulkin kasar Bangladesh inda babban hafsan sojin kasar Waker-Uz-Zaman ya fadi matakin da suka dauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bangladesh - Sojoji sun karbi mulki a kasar Bangladesh bayan murabus din da Firaminista Sheik Hasina ta yi ba zato ba tsammani tare da tserewa daga kasar.

Rahotanni sun ce an sulale da Hasina a cikin wani jirgin sama mai saukar ungulu zuwa Indiya bayan da masu zanga-zanga suka yi wa gidanta kawanya.

Kara karanta wannan

Legas: 'Yan daba sun kai mamaya kusa da ofishin gwamna, an tarwatsa masu zanga zanga

Sojoji sun sanar da karbar mulki a kasar Bangladesh bayan zanga-zanga da ta tsananta
Bangladesh: Firamista ta yi murabus yayin da sojoji suka karbi mulki saboda znaga-zanga. Hoto: @dibang
Asali: Twitter

Zanga-zanga ta barke a kasar a makonnin baya, inda a ranar Lahadin da ta gabata aka kashe akalla mutane 96 daga cikin masu zanga-zangar, inji rahoton Washington Post.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanga-zanga ta tsananta a kasar Bangladesh

Zanga-zangar da aka shafe makonni ana yi a cikin watanni biyun da suka gabata, ta yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 260.

An kashe mutanen ne biyo bayan matakin da jami'an tsaro suka dauka kan masu zanga-zangar da suka nuna adawa da rusa wasu bangarori na ayyukan jama'ar kasar.

Kotun kolin kasar ta soke wannan hukuncin wanda ya kai ga dakatar da zanga-zangar na wucin gadi, kafin zanga-zangar ta sake barkewa a ranar Lahadi.

Sojoji sun karbi mulki a Bangladesh

Tashar France 24 ta ruwaito babban hafsan sojin kasar, Waker-Uz-Zaman ya yi jawabi ga al'ummar kasar, yana mai cewa mulkin soja zai zama wani mataki na wucin gadi kawai.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta ci shugabar kasa, Firayim Minista ta tsere da aka zagaye fadar ta

"Kasar ta sha wahala da yawa, tattalin arziki ya tabarbare, an kashe mutane da yawa - lokaci ya yi da za a dakatar da tashin hankali."

- Janar Waker-Uz-Zaman.

Akalla mutane 66 ne aka kashe a ranar Litinin, in ji ‘yan sanda, inda suka ce gungun ‘yan daba sun kaddamar da harin ramuwar gayya kan abokan kawancen Hasina.

Sojoji za su hukunta masu zanga-zanga

A wani labarin, mun ruwaito cewa babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce sojoji za su shiga tsakani idan masu zanga zanga suka ci gaba da keta doka.

Janar Christopher Musa ya bayyana cewa idan suka fahimci lamarin ya sha kan ƴan sanda, za su kawo ɗauki domin tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.