Darajar Najeriya Ta Kara Sama a Saudiyya, Mahajjaci Ya Mayar da Kudin Tsintuwa
- Wani mahajjacin Najeriya ya kara mayar da makudan kudi da ya samu a Makka ga hukumar kula da mahajjata ta kasa (NAHCON)
- Hakan na zuwa ne bayan wani mahajjacin daga garin Limawa na jihar Jigawa ya mayar da kudin tsintuwa a makon da ya wuce
- Shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), Malam Jalal Ahmad Arabi ya jinjinawa mahajjacin bisa halin da ya nuna
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia - Wani mahajjacin Najeriya ya yi abin kirki na mayar da makudan kudin da ya tsinta.
Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan wani mahajjacin daga jihar Jigawa ya mayar da makudan kudin tsintuwa a kasa mai tsarki.
Legit ta tabbatar da labarin ne a cikin sakon da hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nawa mahajjacin Najeriyan ya tsinta?
Hukumar NAHCON ta tabbatar da cewa mahajjacin ya samu kudin tsintuwa da suka kai €1,750 a garin Makka.
Bincike ya nuna cewa idan ka mayar da kudin da mahajjacin ya tsinta zuwa Naira za su kai kusan Naira miliyan 2.8.
Daga wace jiha mahajjacin ya fito?
Rahotanni sun nuna cewa mahajjacin mai suna Muhammad Na'Allah ya fito ne daga jihar Zamfara, rahoton Vanguard.
Har ila yau, an bayyana cewa Muhammad Na'Allah dan asalin karamar hukumar Gummi ne a jihar ta Zamfara.
NAHCON ta yabi Muhammad Na'Allah
Shugaban hukumar HAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi ya ce lallai Muhammad Na'Allah ya yi abin kwarai.
Malam Jalal Ahmad Arabi ya kara da cewa Muhammad ya amsa cewa shi na Allah ne a aikace ba a suna kawai ba.
Gwamna ya yi korafi kan NAHCON
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya nuna takaicinsa kan yadda hukumar NAHCON ta tafiyar da ayyukan Hajjin bana na shekarar 2024.
Gwamna Bago ya yi kira ga majalisar tarayya da ta binciki tallafin N90bn da gwamnatin tarayya ta bayar domin gudanar da aikin Hajjin bana.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng