Abin Farin Ciki: Wata Ƙasar Afrika Ta Fara Haƙo Mai a Karon Farko, an Samu Bayanai

Abin Farin Ciki: Wata Ƙasar Afrika Ta Fara Haƙo Mai a Karon Farko, an Samu Bayanai

  • Shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya yi magana kan abin da zai yi da ribar da ake samu daga siyar da mai da iskar gas
  • Wannan na zuwa ne bayan da kamfanin Woodside ya fara hako mai daga gabar tekun Sangomar da ke Senegal a karon farko a tarihi
  • Ana dai sa ran Senegal za ta iya hako ganguna 100,000 zuwa 120,000 na gas da danyen mai a kullum wanda zai gyara tattalin arzikinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bayan tsaikon da aka yi na tsawon shekaru, kamfanin Woodside ya ce ya fara hako mai daga gabar tekun Sangomar, mai tazarar kilomita 100 kudu daga Dakar babban birnin kasar Senegal.

Kara karanta wannan

Super Eagles: Najeriya za ta dauƙo hayar koci daga kasar waje, Finidi George ya gaza

Tashar hako man ta na da damar ajiyar ganga miliyan 1.3, kuma ana sa ran za ta iya hako ganga 100,000 zuwa 120,000 na gas da danyen mai a kullum.

Kasar Senegal ta fara hako mai
Kasar Senegal ta shiga jerin kasashe masu arzikin mai. Hoto: @PR_Diomaye
Asali: Getty Images

Kyakkyawan fatan da Senegal ke yi

Jaridar RFI ta ruwaito cewa Senegal na da kyakkyawan fata kan asana'antar mai da iskar gas ta kasar duk da sanin cewa ba za ta kai manyan kasashe masu hako mai kamar Najeriya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da hakan, ana sa ran masana'antar za ta kawo wa Senegal kudaden shiga na biliyoyin daloli da kuma bayar da gudummawa wajen kawo sauyi ga tattalin arzikinta.

Daraktan kamfanin kasuwanci na Afirka, BNG, Charles Thiemele ya bayyana cewa:

“Fara hako mai a kasar labari ne mai dadin gaske. Wannan ya tabbatar da nasar shekarun da aka shafe ana neman mai a kasar.

Kara karanta wannan

NELFUND ta fadi daliban da su ka cancanci lamunin karatu

"Sarrafa mai a kasar zai taimaka wajen rage yawan kudaden da take kashewa wajen makamashi, wanda ya haifar da matsalolin kasafin kudi da dama."

- Charles Thiemele

Bassirou ya bayyana mataki na gaba

Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya ce kasar za ta tabbatar ta yi amfani da ribar da ake samu daga siyar da mai da iskar gas ta yadda ya kamata, in ji rahoton BBC.

Mista Faye, wanda aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a watan Afrilu, ya yi karfafa shirin hako man a wani bangare na sauye-sauyen da ya yi alkawari a lokacin yakin neman zabe.

Da yake magana da daliban a ranar Talata, ya ce an kafa “asusun jama’a” domin amfanin yara manyan gobe, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

Bassirou Faye ya kafa tarihi a Afrika

A wani labarin, mun ruwaito cewa Bassirou Diomaye Faye ya kafa tarihi a Afrika bayan da ya zama zababben shugaban kasa da karancin shekaru.

Kara karanta wannan

"Duk da masu ja da ikon Allah, mun yiwa mutanen Kano aiki," Gwamna Abba gida gida

Rahotanni sun bayyana cewa Bassirou Faye, mai shekaru 44 ya samu tazarar kuri'u mai yawa a zaben shugaban kasar Senegal da ya gudana a watan Afrilu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.