Saudiyya Ta Tsaurara Tsaro, Ta Yi Albishir Ga Mahajjata Yayin da Aikin Hajji Zai Kankama

Saudiyya Ta Tsaurara Tsaro, Ta Yi Albishir Ga Mahajjata Yayin da Aikin Hajji Zai Kankama

  • Kasar Saudiyya ta sanar da kammala shirye-shiryen samar da isasshen tsaro domin kare mahajjata a yayin gudanar da Hajjin bana
  • Ministan harkokin cikin gida, Abdulaziz bin Saud ne ya tabbatar da haka yayin wani atisaye da jami'an tsaron kasar suka gudanar
  • Ministan ya kuma tabbatar da matakan tsaro da kasar ta ƙara dauka a asibitoci domin kara tsaro da kiyaye lafiyar mahajjata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia - Kasar Saudiyya ta ce ta shirya tsaf domin samar da wadataccen tsaro ga mahajjata da suka isa kasar domin aikin Hajji.

Kasar ta fitar da sanarwar ne yayin da mahajjata ke kokarin kammala isowa kasar domin fara aikin Hajjin bana.

Kara karanta wannan

Duk da dokar hana masu ciki aikin Hajji, Hajiyar Najeriya ta haifi jaririn farko a Makkah

Saudiyya
Jami'an tsaro sun yi atisaye domin fara aikin Hajji a Saudiyya. Hoto: Inside the Haramain
Asali: Facebook

Jaridar Arab News ta ruwaito cewa ministan harkokin cikin gida, Abdulaziz bin Saud ne ya bayyana lamarin ga manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aikin Hajji: Jami'an tsaro sun yi atisaye

Yayin da mahajjata ke kokarin kammala isowa kasar Saudiyya, jami'an tsaron kasar sun yi atisaye domin nuna suna zaune kan shiri.

Jami'an tsaron sun yi fareti da nuna dabarun yaki kala-kala ciki har da baje kolin yadda ake aiki da motocin sulke da jiragen sama.

Bayanin ministan Saudiyya kan hajjin bana

A yayin atisayen, ministan harkokin cikin gida, Abdulaziz bin Saud ya tabbatar da cewa kasar ta kammala shirye shirye domin fuskantar dukkan kalubalen tsaro.

Abdulaziz bin Saud ya ce suna yiwa mahajjata albishir da cewa za su yi aikin Hajji cikin sauki da aminci a kasar, rahoton Saudi Gazette.

Saudiyya ta kara tsaro a asibitoci

Kara karanta wannan

Tsananin zafi: Matakan da Saudiyya ta dauka domin rage mutuwar mahajjata

Har ila yau, ministan ya halarci taron kiwon lafiya na farko da aka gabatar a kasar domin ba da kulawa cikakkiya ga lafiyar mahajjata.

Ministan ya tabbatar da kara jami'an tsaro a asibitoci, fadada wuraren karbar magani da asibitoci da kuma yin amfani da na'urar zamani domin inganta lafiyar mahajjata.

An kama 'yan damfara a Saudiyya

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Saudiyya ta kama yan damfara hudu masu amfani da yanar gizo domin cutar mahajjata da sauran al'ummar kasar.

Rahotanni sun nuna cewa an kama mutanen dauke da na'ura mai ƙwaƙwalwa, tarin wayoyin hannu, layukan waya da dama da sauran kayan da suke amafani da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel