Kasar Saudiyya Ta Dauki Tsauraran Matakai Kan Masu Zuwa Hajji Ta Barauniyar Hanya
- Hukumomin kasar Saudiyya sun bayyana tsauraran matakan hana masu zuwa aikin Hajji ta barauniyar hanya
- Gwamnatin kasar ta ce akwai tara mai tsanani ga dukkan wanda aka kama yana aikin Hajji ba tare da izini daga hukuma ba
- Dadin dadawa, hukumomi sun tabbatar cewa hukuncin zai shafi dukkan wanda aka kama, dan kasa ne ko ba dan kasa ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia - Hukumomin kasar Saudiyya sun dauki mataki mai tsanani kan masu zuwa aikin Hajji ba tare da izinin gwamnatin kasar ba.
A cikin sanarwar da kasar ta fitar, ta tabbatar da cewa da 'yan kasa da baki duk za su shiga karkashin hukuncin.
Rahoton da jaridar Daily Trust ta fitar ya nuna cewa kasar ta fitar da dokar ne domin rage cunkoso da ake samu yayin aikin Hajji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hajji: Taran da Saudiyya ta lafta
Ma'aikatar Hajji da Umra ta Saudiyya ta sanar da cin taran Riyal 10,000 wanda yayi daidai da N3,991,170 ga duk wanda aka kama ya shiga filin aikin Hajji ta barauniyar hanya a karon farko.
Idan kuma aka kara kama mutum hukumomi sun ce za a ci taransa har Riyal 100,000 wanda ya haura N39m a kudin Najeriya.
Yaushe dokar za ta yi aiki a Sadiyya?
Hukumomin kasar sun tabbatar da cewa dokar za ta yi aiki ne tsakanin 2 ga watan Yuni zuwa 20 ga watan nan na 2024.
A tsakanin lokacin duk wanda aka kama ko bako ko dan kasa a filin aikin Hajji ba tare da izini ba dokar za ta yi aiki a kan sa.
Wuraren da dokar za ta yi aiki
Kasar ta ware wurare na musamman da duk wanda ya shiga ba tare da izini ba, doka za ta hau kansa.
Wuraren sun hada da cikin Makka, Mina, wuraren taruwar mahajjata da tashar jirgin kasan Rusayfah.
Saboda haka hukumar alhazai ta kasa ta gargadi 'yan Najeriya kan cewa kada su yi wasa da katin shaida da za a raba musu domin kaucewa fushin doka, rahoton the Cable.
Gwamnan Yobe ya ba alhazai kyauta
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Yobe karƙashin Gwamna Mai Mala Buni ta cika alƙawarin da ta ɗauka na tallafawa alhazan jihar 1,332.
Shugaban hukumar jin daɗin alhazai na jihar, Alhaji Mai Aliyu ya ce kowane mutum ɗaya daga cikin mahajjatan ya samu alawus na N135,000.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng