Rupert Murdoch: Bayan Rabuwa da Matarsa, Attajiri Mai Shekara 93 Ya Angonce a Karo na 5
- A karo na biyar, shararraen mai kudin nan Rupert Murdoch dan shekaru 93 ya angwance da amaryasa, Elena Zhukova mai shekaru 67 a Beil Aeir
- Ya auri matarsa a kayataccen gidansa da ke California jim kadan bayan ya haduwarsa a wani taro da tsohuwar matarsa 'yar asalin kasar China Wendi
- Mista Murdoch, wanda yanzu haka ke da yara shida shi ne shugaban Kamfanin labarai na News Corporation, mamallakan Fox News Wall Street Journal
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
California- Shahararren mai kudin nan, kuma shugaban manyan kamfanonin yada labarai a duniya, Rupert Murdoch ya angwance a karo na biyar.
Attajirin mai shekaru 93 ya angwance da amaryarsa, da ta kware a fannin ilimin halitta Elena Zhukova mai shekaru 67 a gidansa da ke birnin California.
BBC ta wallafa cewa ya hadu da amaryarsa jim kadan bayan soke baikonsa da wata matar Ann Lesley Smith a watan Afrilun 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Murdoch da Zhukova suka hadu
Vanity Fair ta bayyana cewa attajirin ya hadu da amaryarsa wani taro da tsohuwar matarsa ta uku, Wendi Deng ta shirya.
A shekarar da ta gabata ne Murdoch ya sauka daga mukamin shugaban kamfanin yada labarai na Fox and News Corp da aka fi kallo a kasar Amurka, ya bar daya daga ‘ya’yansa ya ci gaba da shugabantar kamfanonin.
Rupert Murdoch ya yi auren karshe?
Kafin angwancewa da Zhukova, Murdoch ya taba auren wata mai aiki a kamfanin jirgin sama, Patricia Booker, yar jarida Anna Mann da yar fim Jerry Hall.
Rupert Murdoch yana fatan Elena Zhukova ta zama matarsa ta karshe da zai samu soyayyar da yake bukata a wajenta.
Kotun Amurka na neman Abba Kyari
A wani labarin kun ji wata kotu dake zamanta a kasar Amurka ta nemi a kamo mata dan sandan kasar nan Abba Kyari domin amsa wadansu tambayoyi.
Otis Wright na kotun Amurka na jihar California ta bukaci a kamo Kyari ne domin amsa tambayoyi kan laifin da Ramon Abbas da aka fi sani da Hushpuppi ya aikata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng