Tausayin Falasɗinawa Ya Sa Sojan Kasar Amurka Yin Ritaya Daga Aikin Tsaro
- Wani babban sojan Amurka mai suna Harrison Mann ya ajiye aikinsa domin nuna adawa ga kisan da ake yi wa Falasɗinawa
- Sojan ya aika sakon ajiye aikin ne a watan Nuwamban shekararar 2023 zuwa ga hukumar leken asirin kasar Amurka
- A cikin wasikar, Manjo Mann ya bayyana alakarsa da Yahudawa tare da faɗin dalilan da suka sanya shi ajiye aikin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Babban sojan Amurka, Manjo Harrison Mann ya ajiye aikinsa domin nuna goyon bayan Falasɗinawa.
Manjo Mann ya nuna cewa goyon bayan da Isra'ila ke cigaba da samu wurin Amurka abin Allah wadai ne.
Dalilin ajiye aikin Manjo Mann a Amurka
Rahoton jaridar Al-Jazeera ya nuna cewa sojan ya zargi kasar Amurka da nuna jin dadi kan kisan gilla da Isra'ila ke yi ga fararen hula a Gaza.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ajiye aiki da sojan ya yi ya kara adadin ma'aikata da suka yi murabus a Amurka domin nuna goyon baya ga Falasɗinawa.
Manjo Mann ya bayyana ajiye aikin ne cikin wata wasika da ya rubuta wa hukumar leken asirin Amurka.
Yaushe Manjo Mann ya ajiye aikin soja?
Jami'in ya rubuta wasikar ne ta hannun wani abokinsa da ke aiki a hukumar a watan Nuwamban shekararar da ta gabata.
Babban sojan ya kuma bayyana rashin imani da tausayi da kasar Amurka ke nunawa a matsayin dalilin ajiye aikin da ya yi.
A cewar Manjo Mann, abin takaici ne ga Amurka a ce tana taimakawa wajen azabtar da yara da mata da ke Gaza da kewaye.
Alakar Manjo Mann da Yahudawa
Sojan ya kara da cewa a matsayinsa na wanda ya hada jini da Yahudawa ya san Allah yana fushi da yin kisan kare dangi, rahoton Aminiya.
Sauran sojojin da suke aiki tare sun nuna goyon baya a kan matakin ba babban sojan ya dauka.
Shi'a ta yi zanga-zanga saboda Falasdinawa
A wani rahoton, kun ji cewa wasu gungun mabiya aƙidar shi'a a Najeriya sun fito tattakin nuna goyon baya ga Falasɗinawa bayan sabon yaƙin da ya ɓarke.
Malamin Shi'ah Sheikh Sidi Munir Sokoto, ya ce ƙungiyar Shi'a IMN karkashin Sheikh Zakzaky ya saba gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng