Lebanon: Hizbullah Ta Kai Harin Ramuwar Gayya Kan Kasar Isra’ila
- Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta ce ta harba makaman roka na Katyusha da Falaq da dama a Kiryat Shmona da ke arewacin Isra'ila
- Hizbullah ta ce ta harba rokokin ne a matsayin martani ga mummunan harin da Isra'ila ta kai a Mais al-Jabal, da ke kudancin Lebanon
- Kungiyar ta Lebanon ta sha bayyana cewa tsagaita bude wuta a Gaza ne kawai zai kawo karshen hare-haren da take kaiwa Isra'ila
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kasar Lebanon - Isra'ila da kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon da ke samun goyon bayan Iran suna ci gaba da yin musayar wuta akai-akai a kan iyakokin kasashen biyu.
Wannan na zuwa ne tun bayan harin da kungiyar Hamas ta Falasdinu ta kai wa kudancin Isra'ila a watan Oktoba wanda ya haifar da yakin Gaza, rahoton jaridar RFI.
Fada ya kara tsananta a cikin 'yan makonnin nan, inda Isra'ila ta kai hare-hare a cikin kasar Lebanon, yayin da kungiyar Hizbullah ke mayar da martani a kan sojin Isra'ila.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Isra'ila ta kai hari kudancin Lebanon
Wata kafar yada labaran kasar Labanon ta ce wani harin da Isra'ila ta kai a wani kauye da ke kudancin kasar a ranar Lahadin da ta gabata, ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
An bayyana mamatan a matsayin namiji, mace da ’ya’yansu masu shekaru 12 da 21, sannan ta ce wasu mutane biyu sun samu raunuka, jaridar AlJazeera ta ruwaito.
Wata majiyar tsaron Lebanon, wadda ta bukaci a sakaya sunanta saboda ba su da izinin yin magana da manema labarai, ta tabbatar da harin ya kashe “farar hula hudu”.
Tun da farko shugaban karamar hukumar Mais al-Jabal Abdelmoneim Shukair ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa an kashe ma'aurata da 'yayansu.
Hizbullah ta harba rokoki kan Isra'ila
A cikin wata sanarwa da kungiyar Hizbullah ta fitar ta ce ta harba makaman roka na Katyusha da Falaq da dama a Kiryat Shmona da ke arewacin Isra'ila.
Channels TV ta ruwaito Hizbullah ta ce ta harba rokokin ne a matsayin ramuwar gayya ga mummunan laifin da Isra'ila ta aikata a Mais al-Jabal.
Kungiyar ta Lebanon ta sha bayyana cewa tsagaita bude wuta a Gaza ne kawai zai kawo karshen hare-haren da take kaiwa Isra'ila, a wani mataki na nuna goyon baya ga Gazan.
Amurka da Faransa dai sun yi kokarin amfani da diflomasiyya domin kwantar da tarzoma a kan iyakar Lebanon da Isra'ila, amma abin ya ci tura.
Muhimman lokuta a yakin Isra'ila da Hamas
Tun da fari, Legit Hausa ta fitar da rahoto kan wasu muhimman lokuta 10 a yakin da yaki ci yaki cinyewa tsakanin Isra'ila da Hamas.
Legit Hausa ta yi nazari kan yadda yakin wata shida ya mayar da yankin Gaza kufai, kuma ya mayar da arewacin kasar ta koma makabartar dubunnan mutane.
Asali: Legit.ng