Akwai Sa Hannun Tsohon Shugaban Kasa a Juyin Mulkin Nijar, Ɗiyar Bazoum

Akwai Sa Hannun Tsohon Shugaban Kasa a Juyin Mulkin Nijar, Ɗiyar Bazoum

  • Watanni bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum a Jamhuriyar Nijar, Hinder, diyar Bazoum ta yi babbar fallasa
  • Hinder, ta zargi tsohon shugaban kasar Nijar, Issoufou Mahamadou da kitsa juyin mulkin da kuma hana sojoji su saki mahaifinta Bazoum
  • Diyar Bazoum ta kuma zargi Issoufou da kokarin komawa kan karagar mulkin kasar idan sojoji sun mika mulkin ga farar hula nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Niger - Hinder, diyar hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, ta yi magana kan juyin mulkin da aka yi a kasar watannin baya.

Hinder, ta zargi tsohon shugaban kasa Issoufou Mahamadou da kitsa juyin mulkin da sojoji suka yi wa mahaifinta Bazoum.

Kara karanta wannan

"Shi ke haukata 'yan kasa", Malamin addini a Kaduna ya ja kunnen Tinubu kan halin kunci

Hinder Bazoum ta yi magana kan juyin mulkin sojoji a Jamhuriyar Nijar
Diyar Bazoum ta zargi tsohon shugaban kasa Mahamadou Issoufou da kitsa juyin mulki a Nijar. Hoto: @IssoufouMhm, @mohamedbazoum
Asali: Twitter

An kama Bazoum da matarsa ​​a fadar shugaban kasa da ke Yamai tun bayan da jami'an soji suka kwace mulki a ranar 26 ga watan Yuli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An zabe shi ne shekaru biyu da suka wuce, inda ya gaji Shugaba Mahamadou Issoufou, a mika mulki na farko da aka yi cikin lumana tun bayan samun ‘yancin kai.

"Issoufou ya kitsa juyin mulkin Nijar" - Hinder

A wata hira da BBC, Hinder ta yi wannan zargin, inda ta ce yau watanni shida ke nan da iyalan Bazoum suka samu labarin iyayensu da halin da suke ciki.

"Abin da ya fi tsaya mana a wuya shi ne gano cewa Mahamadou Issoufou shi ne wanda ya shirya komai saboda son zuciya da kuma kare muradunsa.
“Yana da yi mana matukar zafi idan muka tuna cewa azzaluman da suka yi juyin mulkin mutane ne da muka sani kuma muka yi zumunci da su."

Kara karanta wannan

Shirin ba ɗalibai rancen kuɗi; Tinubu ya naɗa Jim Ovia a matsayin shugaban NELFund

- Hinder Bazoum

"Issoufou ya hana a saki Bazoum" - Hinder

Hinder ta bayyana cewa Mohammadou Issoufou wanda abokin iyayensu ne na tsawon shekaru 33, suna da shaidar cewa shi ne ya hana gwamnatin mulkin soja ta saki mahaifinsu.

"Muna ji muna gani an mayar da mu a marayu, kuma ba wanda muke zargi sai tsohon abokin mahaifinmu, tsohon shugaban Nijar, Mohamadou Issoufou.
"Juyin mulkin zai ba shi damar komawa kan karagar mulki bayan wani gajeren mulki na soja inda za a amince da sabon kundin tsarin mulki a kasar."

- Hinder.

A watan Yuli, Issoufou ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa yana da niyyar tattaunawa da gwamnatin mulkin soja don mayar da Bazoum kan kujerar shugabancin kasar.

Gwamna ya nada kansa kwamishina

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya nada kansa a matsayin kwamishinan filaye, safiyo da tsare-tsare na jihar.

Wannan sanarwar ta bazata na zuwa ne a lokacin da gwamnan ke rantsar da kwamishinonin jihar inda ya ce nada kansa mukamin zai dakile rashawa a ma'aikatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.