ECOWAS Ta Ɗage Takunkumi 8 Da Ta Ƙaƙabawa Jamhuriyar Nijar, Ta Bada Dalili

ECOWAS Ta Ɗage Takunkumi 8 Da Ta Ƙaƙabawa Jamhuriyar Nijar, Ta Bada Dalili

  • Kungiyar ECOWAS karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta dage takunkumin da ta sakawa Jamhuriyar Nijar da sauran kasashen da sojoji ke mulki
  • Hasashe kan rahotanni daga taron da ECOWAS ta yi a ranar Asabar sun nuna cewa an dage takunkumi guda takwas
  • Kungiyar Hadin Kan Kasashen Afirka ta Yamman ta dage takunkumi kan Jamhuriyar Nijar, Burkina Faso da Mali kan dalilai biyu

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

FCT, Abuja - Kungiyar Hadin Kan Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) da Shugaba Bola Tinubu ke yi wa jagoranci ta dage takunkumi kan daya cikin mambanta, Jamhuriyar Nijar.

An rahoto cewa an dauki wannan matakin ne yayin taron shugabannin kungiyan kasashen Afirka ta Yamman da aka gudanar a Abuja ranar Lahadi, 24 ga watan Fabrairu, kan dalilan jin kai.

Kara karanta wannan

Rayuka 7 sun salwanta saboda turmutsitsi a wajen siyan shinkafar kwastam a jihar APC

ECOEWAS ta janye takunkumin da ta dorawa Nijar
ECOWAS ta dauke takunkumin da ta dora wa Nijar. Hoto: Bola Tinubu
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sanar da hakan cikin wani wallafa a manhajar X da TRT Afirka ta yi mai taken "ECOWAS ta dage takunkumi kan Jamhuriyar Nijar da Guinea'. An saka takunkumin ne bayan juyin mulki da sojoji suka yi a kasashen.

Jerin takunkumin da ECOWAS ta dage wa Nijar

An dage takunkumi takwas kuma sune:

1. An dage rufe iyakoki, ciki har da na kasa da sama, tsakanin Nijar da kasashen ECOWAS.

2. An kuma dage takunkumin hana jiragen sama tashi daga Nijar zuwa kasashen ECOWAS.

3. An kuma dage takumkumin hana kasuwanci tsakanin kasashen ECOWAS da Nijar.

4. Kungiyar kasashen Afirka ta Yamman ta dage ayyuka da hada-hadar makamashi da Nijar.

5. Ta kuma dage rufe asusun ajiyar kudi na Nijar da ke dukkan manyan bankunan ECOWAS.

6. An kuma bude dukkan asusun bankunan kasuwanci na Nijar a dukkan manyan bankunan ECOWAS.

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa sun yi martani mai daukar hankali bayan ECOWAS ta cire takunkumi kan Nijar

7. An kuma dage takunkumin hana tallafin kudi da hada-hada da kasashen da ke makwabtaka da Nijar.

8. Kungiyar ta kuma dage takunkumin hana tafiye-tafiye da aka dora wa jami'an sojojin Nijar da iyalan wadanda ke da hannu a juyin mulkin da wadanda suka yarda suka karbi mukami a gwamnatin.

Gidan Talabijin na Najeriya (NTA) a wani wallafa a X ya ce an 'dage takunkumin da aka kakabawa Nijar ne don cigaba da tattaunawa tare da sulhu da Burkinsa Faso, Mali da Nijar da ke shirin ficewa daga ECOWAS.'

Ga wallafar da NTA da TRT suka yi kan lamarin:

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164