Kasashen Mali, Burkina da Nijar Sun Sanar da Ficewarsu Daga Kungiyar ECOWAS

Kasashen Mali, Burkina da Nijar Sun Sanar da Ficewarsu Daga Kungiyar ECOWAS

  • Wasu kasashen Afrika ta Yamma sun bayyana ficewa daga kungiyar ECOWAS ta kasashen Afrika
  • Mali, Burkina Faso da Nijar ne kasashen da ke kai ruwa rana da ECOWAS tun bayan juyin mulkin Nijar
  • Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da juyin mulkin Nijar, ya ce ECOWAS za ta dauki mataki kan hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Kasar Mali - Kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar sun alanta janyewa da ci gaba da zama da mambobin kungiyar Cigaban Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS).

Wannan na zuwa ne a wata sanarwar da manyan jami’an sojojin kasashen suka fitar ta bai daya a gidan talabijin na Mali.

A bangaren Mali, Kanar Abdoulaye Maiga, ministan kula da yankunan kasar ta Mali, kuma kakakin gwamnatin rikon kwaryar kasar ne ya karanta sanarwar.

Kara karanta wannan

Kano: Hukumar Kashe Gobara ta ceto wani matashi da bashin miliyan 2 ya sa zai kashe kansa

Kasashe 3, Mali, Burkina, Nijar sun fice daga kungiyar ECOWAS
Kasashen Afrika uku sun fice daga ECOWAS | Hotuna: GettyImages
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka zo da shawarin

A cewarsa, wannan shawari ne da kasashen suka yanke domin bayyana kasancewarsu kasashe mai cin gashin kansu, Al-Jazeera ta ruwaito.

Hakazalika, ya ce wannan na nufin shugaban kasar Mali, Ibrahim Traore da na Burkina Faso, Kanal Assimi Goita da kuma na Nijar Janar Abdourahamane Tchiani sun daukar aniyar kare kasashensu.

Haka kuma, sun bayyana cewa, za su tabbatar da cimma duk wasu tsammani da kuma samar da duk wani fata na ‘ya’yan kasashen.

Dalilin kirkirar ECOWAS tun da fari

Idan baku manta ba, an kafa ECOWAS ne a 1975 da zimmar habaka tattalin arziki musamman ta fuskar sufuri, masana’antu, sadarwa da makamashi har ma da noma da kasuwanci.

Hakazalika, manufar ECOWAS ce ta samar da hanyoyin habaka harkar ma’adinai, karfin kudi da kuma hanyoyin more rayuwa masi amfani, rahoton France24.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta dauki mummunan mataki kan 'yan bijilanti 5 saboda dalili 1 tak, sun yi martani

Tun bayan yin juyin mulki a Nijar ECOWAS ta bakin shugabanta, Bola Ahmad Tinubu ta yi Allah wadai tare da bayyana yiwuwar daukar mataki.

Kasashen Burkina Faso da Mali ne masu bayyana goyon bayansu kai tsaye ga sojin juyin mulkin Nijar.

Matakin ECOWAS ga juyin mulkin Nijar

A tun farko, shugaban kasa Bola Tinubu ya aike da sako ga majalisar dattawa yana mai sanar da shirin kungiyar kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) na daukar matakai kan jamhuriyar Nijar.

Shugaban ya sanar da Majalisar dokokin kasar cewa ECOWAS na shirin daukar matakin soji da sauran takunkumi kan masu juyin mulki a Jamhuriyar Nijar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.