Babban Malamin Addini Ya Damfari Mabiyansa $1.3m, Ya Bayyana Wanda Ya Ba Shi Umarnin Yin Hakan
- Wani Fasto a Amurka ya ce ya saci dalar Amurka miliyan 1.3 bisa umarnin da ubangiji ya ba shi bayan ya sayar wa jama’arsa wani kirifto marar amfani
- Ofishin babban mai shari’a na Colorado ya tuhumi Eli Regalado da matarsa Kaitlyn da laifin zamba bayan sun yi iƙirarin samun umarnin daga Allah
- Regalado ya amince da aikata laifin sannan ya ce wasu daga cikin kuɗaden da aka samu sun tafi wajen gyaran gidansa, wanda ya ce Allah ya umarce shi da yin hakan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Amurka - Wani fasto a Amurka, Eli Regalado da matarsa, Kaitlyn, a halin yanzu suna fuskantar shari’a kan zargin sayar da wani kirifto da ake kira INDXcoin ga Kiristoci a Colorado, tare da da ba su tabbacin cewa za su yi arziki.
A cewar jaridar The Guardian, mai binciken ya ce ya gano cewa mutane 300 ne suka zuba jarin dala miliyan 3.2 a cikin abin da Regalado da matarsa suka yi iƙirarin cewa umarni ne daga Allah.
Wannan yana ƙunshe ne a cikin ƙorafin da ofishin babban lauyan jihar Colorado ya shigar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Faston Amurka ya sayar da kirifto na ƙarya ga mabiyansa
Faston da matarsa, waɗanda ke gudanar da cocin yanar gizo, ba su da gogewa a harkar kirifto.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar da ke kula da kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Colorado ta fitar.
Da yake magana kan zarge-zargen da ake yi masa na zamba, faston ya nanata ƙudurinsa na aiwatar da abin da Allah ya ce ya yi.
Ina ya kai kuɗaden?
Ya kuma bayyana cewa an yi amfani da wasu kuɗaden wajen gyara gidansa, wanda ya ce yana daga cikin umarnin da aka ba shi daga sama.
A cikin bidiyon da aka buga akan shafin INDXcoin, Regalado ya ce:
"A cikin wannan dala miliyan 1.3, rabin dala miliyan sun tafi wurin IRS, kuma wasu dala 100,000 sun tafi wajen gyaran gida da Ubangiji ya ce mu yi."
Kalli bidiyon a nan ƙasa:
Fasto Ya Umarci Mabiyansa Su Ba Shi Albashinsu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Fasto Anosike ya shaida wa mabiya cocinsa cewa albashinsu na watan Janairu na shi ne ba na coci ba.
Faston ya yi iƙirarin cewa ba ya tsoron gutsiri tsoma da sukar mutane, yana mai jaddada cewa albashinsu na farko a 2024 nasa ne kawai.
Asali: Legit.ng