Allahu Akbar: Bidiyon Yadda Limami Ya Rasu Yana Tsaka da Jan Sallah a Masallaci Ya Dauki Hankali

Allahu Akbar: Bidiyon Yadda Limami Ya Rasu Yana Tsaka da Jan Sallah a Masallaci Ya Dauki Hankali

  • An ga wani bidiyon da ke nuna yadda wani limami ya yi kyakkyawar karshe yana tsaka da sallah a wani masallacin Indonesia
  • Bidiyon ya nuna lokacin da bawan Allah ya kwanta dama a lokacin da ya kai sujjada, wacce ta kasance ta karshe kenan a rayuwarsa
  • Jama’a a kafar sada zumunta ta Twitter sun masa fatan cikawa imani da kuma roka masa gafara da aljanna mai girma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Kasar Indonesia - Wani al’amari mai taba zuciya ya auku a kasar Indonesia, inda wani limami ya rasu yana tsaka da sallah tare da mamu a wani masallaci.

A bidiyon da Legit Hausa ta samo, an ga lokacin da limamin ya tada raka’a, har ta kai ga ya yi sujjuda, sujjadar karshe kenan a rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Kwamitin Tinubu ya waiwayi masu kudi, ana shirin laftawa attajirai haraji

A cewar Abdulfatah Ayofe, wani ma’abocin Twitter da ya yada bidiyon a shafinsa, lamarin ya auku ne a ranar 2 ga watan Janairun wannan shekarar da muka shiga.

Limami ya mutu yana tsaka da sallah
An ga yadda limami ya mutu yana tsaka da sallah | Hoto: GettyImages, @abdullahayofel (X)
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A addinin Islama, alama ce ta rahama da kyakkayawar karshe Musulmi ya cika a lokacin da yake tsaka da sallah.

Ya aka kare sallar?

A daidai lokacin da mamunsa suka fahimci akwai matsala kasancewar ya jima bai taso ba a sujjadar, sai wasu suka tashi.

Nan ne wani ya gaggauta wucewa domin karasa sallar da aka fara, wacce alamu ke nuna ta farilla ce.

Mutane da yawa a kafar sada zumunta sun mika sakon ta’aziyya tare da yi masa addu’ar Allah ya gafarta masa ya kuma sanya aljanna ce makamarsa.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a a kafar Twitter

Ga kadan daga abin da mutane ke cewa na fata mai kyau da nema masa rahama:

Kara karanta wannan

'Ki ba ni Lokacinki': Bidiyon wakar Abdul D One da ya jawo ce ce ku ce a soshiyal midiya

@iQMike_:

“Allah madaukaki ya mana arziki da kyakkyawar karshe.”

@Teesaids:

“Kyakkyawar karshe itace cikawa da sallah ga kowa.”

@alfatunde:

“Allahu Akbar. Ina lilahi wa. Ina ilaehi rajihuna.”

@taoheed1:

“Allah ya albarkace da kyakkyawar karshe ya kuma karbe mu a matsayin salihan bayinsa, Amin.”

Yadda wani ya mutu a hanyar dawowa daga sallar idi

A wani labarin, abin bakin ciki ya faru a Ilorin, Jihar Kwara, a ranar Juma'a, a lokacin da wani mutum mai matsakaicin shekaru ya rasa ransa sannan wasu uku suka jikkata sakamakon hatsarin mota.

Hatsarin da aka rahoto ya ritsa da mutane hudu ne da suke kan babur ne a hanyarsu na dawowa daga Sallar Idi a ranar Juma'a a Ilorin, The Punch ta rahoto.

Sauran mutane ukun da ke kan babur din, wacce ta yi karo da motar, sun samu munanan rauni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.