Juyin Mulki: Majalisar ECOWAS Ta Nemi a Dage Takunkumin Da Aka Sakawa Nijar
- An yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran shugabannin Kungiyar Hadin Kan Kasashen Afirka (ECOWAS) su dage takunkumin da suka sakawa Jamhuriyar Nijar
- Wasu daga cikin yan Majalisar ECOWAS ne suka yi wannan kirar a ranar Talata, 22 ga watan Nuwamba
- Sai dai, Mai shari'a Edward Amoako Asante, shugaban kotun ECOWAS, ya yi kira da cewa a dauki matakin soji kan sojojin juyin mulkin na Nijar
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Majalisar kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta yi kira ga shugabannin kasashe da gwamnatocin yankin su dage takunkumin da suka sakawa Jamhuriyar Nijar.
Shugaban ECOWAS a watan Yuli ya kakaba takunkumi kan Jamhuriyar Nijar sakamakon hambarar da Mohamed Bazoum da wasu sojoji suka yi karkashin Janar Abdourahamane Tchiani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bulaliyar Majalisar Dattijan Najeriya, Sanata Ali Ndume, wanda ya yi magana da manema labarai bayan taron, ya ce kasashe kimanin bakwai da ke makwabtaka da Nijar suna fuskantar matsala saboda takunkumin, rahoton The Nation.
Ndume ya ce:
"Mata da kananan yara sun fada cikin wahala. Ba a samu wani cigaba ba dangane da warware matsalar nan. Muna kira ga jihohin ECOWAS su dage takunkumin kuma su bude iyakokin Najeriya da Nijar domin talakawa ke shan wahala. Wannan shawara ne da wasu yan kasa da suka damu da abin suka cimma.
"An yi taron ne kawai domin kira ga shugabannin kasashen da ke ECOWAS su duba halin da al'umma suka shiga su kuma warware lamarin Nijar a siyasance."
Juyin mulki: Kotun ECOWAS ta bukaci a dauki matakin soji nan take kan Nijar
Sai dai, a yayin bude taron karo na 2 na majalisar, Mai Shari'a Edward Amoako Asante, shugaban Kotun ECOWAS, ya yi rokon a dauki matakin soji nan take domin magance yawaita juyin mulkin da sojoji ke yi wa shugabannin dimokradiyya a Afirka.
Da ya ke jawabinsa, Mai shari'a Asante ya nuna damuwarsa kan matsalolin da juyin mulkin da sojoji ke janyowa ga dimokradiyya da zaman lafiya.
Ya ce:
"Wadannan kutsen ba wai kawai suna nuna nakasu ga dimokuradiyyarmu bane ba, amma ya kamata ya kalubalanci mu da mu yi tunani kan inda dimokradiyyarmu ke tafiya mu gani ko yana iya samar da kyakkyawan shugabanci wanda zai biya bukatun zamantakewa da tattalin arzikin jama'armu."
Mai shari'a Amoaka Asante ya yi kira ga Majalisar ECOWAS ta duba wannan batun mai muhimmanci, yana mai cewa akwai bukatar a kawo sauye-sauye da za su inganta dimokradiyya a yankin Afirka ta Yamma baki daya.
Ya yi kira ga majalisar ta hada kai da wasu takwarorinta domin tabbatar da aiwatar da manufofinta, na inganta shari'ar da kare hakkin bil-adama.
Nijar: ECOWAS Ta Yi Sabon Magana Kan Yanayin Da Shugaba Bazoum Da Dansa Ke Ciki
A wani rahoton a baya ECOWAS ta yi karin bayani kan halin da hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum da dansa suke ciki.
Kwamishinan ECOWAS na harkokin siyasa, tsaro, da zaman lafiya, Ambasada Abdel-Fatau Musah, ya ce Bazoum da dansa suna cikin mummunan yanayi a tsare a hannun masu juyin mulki.
Asali: Legit.ng