Mutane 37 Sun Mutu Wurin Neman Shiga Aikin Soja a Kasar Congo

Mutane 37 Sun Mutu Wurin Neman Shiga Aikin Soja a Kasar Congo

  • Akalla matasa 37 ne rahotanni suka bayyana sun mutu sakamakon wani turmutsutsu da ya barke a filin wasa na Brazzaville, babban birnin Jamhuriyar Congo
  • Matasan sun je filin ne domin a tantance su a wani shiri da hukumar sojin kasar ke yi na daukar matasa 1,500 aiki, lamarin da ya jikkata mutane da dama
  • Har yanzu ba a samu cikakken rahoton yadda lamura suka faru a wajen ba, sai dai Firayim Minista Anatole Collinet Makosso ya kira lamarin "mummunan iftila'i"

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Brazzaville, Jamhuriyar Congo - Matasa 37 ne suka mutu sakamakon turmutsitsin da ya barke a cikin dare a yayin da hukumar sojin kasar ke shirin daukar aikin soja a wani filin wasa da ke Brazzaville, babban birnin Jamhuriyar Congo, a cewar wata sanarwa a ranar Talata.

Kara karanta wannan

An sake kama hatsabibin dilallin kwayoyi shekaru 7 bayan tserewarsa daga gidan yari a Abuja

A makon da ya gabata, sojojin kasar da aka fi sani da Congo-Brazzaville, sun sanar da daukar matasa 1,500 aikin soja, amma masu shekaru tsakanin 18 zuwa 25.

Congo-Brazzaville
Sojojin kasar da aka fi sani da Congo-Brazzaville, sun sanar da daukar matasa 1,500 aikin soja, amma masu shekaru tsakanin 18 zuwa 25. Hoto: Olivia Acland/Reuters
Asali: UGC

Firayim Minista Anatole Makosso ya magantu kan iftila'in

Reuters ta ruwaito Firayim Minista Anatole Collinet Makosso ya ce mutane 37 ne suka mutu a cikin "mummunan iftila'i," yayin da wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba suka jikkata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An kafa kwamiti kan lamarin bisa sahalewar firayim ministan kasar".

A cewar sanarwar.

An umurci wadanda ke son shiga aikin sojan da su je filin wasa na Michel d'Ornano da ke tsakiyar Brazzaville, rahoton jaridar Aljazeera.

Abin da ya faru a filin wasan har ya yi ajalin matasan

A cewar mazauna yankin, mutane da dama na cikin filin wasan a daren ranar Litinin, lokacin da aka fara turereniya.

Kara karanta wannan

Hadiman 'yan majalisar dokokin Najeriya sun koka kan rashin biyansu albashin watanni 15

Wasu mutane ne suka yi yunkurin bi ta kofar shiga filin ta karfin tsiya, lamarin da ya jawo aka tattake mutane da dama a wajen, kamar yadda mazauna garin suka ce.

Har yanzu ba a samu cikakken rahoton yadda lamura suka faru a wajen ba kuma jaridar AFP ta kasa tantance cikakkun bayanan da kanta.

Yadda ’yan Najeriya za su iya yin karatu kyauta a kasar Faransa

Ofishin jakadancin Faransa, ya sanar da fara karbar takardun 'yan Najeriya masu sha'awar yin karatun digiri na biyu a fannoni daban-daban na ilimi a kasar.

Legit Hausa ta fahimci cewa, ana karbar takardar shaidar kammala karatun HND a shirye-shiryen da mutum zai nema.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.