Antonio Guterres Ya Soki Isra'ila Kan Hare-haren da Su Ke Kai Wa gaza
- Yayin da ake ci gaba da gwabza yaki tsakanin Isra'ila da Hamas, Majalisar Dinkin Duniya ta yi martani
- Sakataren Majalisar, Antonio Guterres ya zargi Isra'ila da saba dokokin kasa da kasa na jin kai a harin da su ke kai wa
- Ya bukaci dukkan bangarorin biyu da su bi dokokin kasa da kasa tun da dukkansu ba su fi karfin doka ba
New York, Amurka - Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antoni Guterres ya zargi Isra'ila da keta hakkin dan Adam a harin da su ke kai wa Gaza.
Guterres ya bayyana haka ne a babban taron mambobin majalisar kan tsaro a birnin New York na Amurka.
Wane zargi Guterres ke yi wa Isra'ila?
Ana ta cece-kuce kan take hakkin jin kai na dan Adam bayan Isra'ila ta datse ruwa da wata da kuma man fetur.
Bashin $3.5bn: Tinubu Ya Fadi Yadda Zai Kasafta Kudaden Don Amfanar Talakawa, Ya Fadi Tsawon Lokacin Biya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan kungiyar Hamas ta kai wani harin bazata kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, cewar Daily Trust.
Daga bisani Isra'ila ta rinka kai munanan hare-hare kan Gaza ta sama da kasa a kokarin harin ramuwar gayya.
Kasashen Amurka da Faransa da Ingila da Jamus da Canada da kuma Italiya sun gargadi Isra'ila kan rashin mutunta dokokin kasa da kasa.
Sai dai sun ce Isra'ila ta na da damar kare kanta daga harin ta'addanci daga kungiyar Hamas ta Falasdinu, Euronews ta tattaro.
Guterres ya ce babu wane bangare daga cikin ma su rikicin da yafi karfin dokar kasa da kasa don haka dole su mutunta doka.
Wane gargadi Guterres ya yi ga Isra'ila, Gaza?
Ya ce:
"Ina matukar jin takaici yadda mu ke ganin take hakkin jin kai na kasa da kasa da ke faruwa a Gaza.
"Babu wani abu da zai halatta raunata mutane ko kashe su da garkuwa da su da kuma harba makamin roka kan jama'a."
Ya ce Falasdinawa sun sha bakar wahala na tsawon shekaru 56, tattalin arziki ya lalace ba su da wata dama ta gyara siyasa da rayuwarsu.
Sai dai ya ce dukkan wadannan matsalolin ba su kai a halatta harin da kungiyar Hamas ta ke kai wa ba, dole ko wane bangare ya bi dokokin kasa da kasa.
Fasto ya gargadi 'yan uwansa masu yi wa Isra'ila addu'a
Kun ji cewa, wani Fasto Chukwuemeka Odumeji ya gargadi sauran Fastocin Najeriya da ke yi wa Isra'ila addu'a da su guji yin haka.
Ya yi barazanar mayar da su makafi da kurame idan ba su fita wannan sha'ani na Isra'ila ba.
Asali: Legit.ng