Nijar Ta Umarci Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya Ta Fice Daga Kasar Cikin Sa'o'i 72

Nijar Ta Umarci Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya Ta Fice Daga Kasar Cikin Sa'o'i 72

  • Yayin ake ci gaba da zaman dar-dar, sojin Nijar sun umarci wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta fice daga kasar
  • Sojin sun bai wa jami'ar jin kai ta majalisar, Louise Aubin sa'o'i 72 da ta fice ta ko wane hali
  • Wannan na zuwa ne bayan Faransa ta fara kwashe dakarunta da duk jami'anta daga kasar a jiya Talata 10 ga watan Oktoba

Yamai, Nijar - Sojin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun fatattaki wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya, Louise Aubin daga kasar.

Nijar ta bai wa Aubin wa'adin sa'o'i 72 da ta fice daga kasar inda su ka ce idan ta saba za su dauki matakin da ya dace a kai, cewar Reuters.

Nijar ta sallami wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya daga kasar
Nijar Ta Sallami Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya. Hoto: Janar Tchiani.
Asali: Getty Images

Meye sojin Nijar su ka ce kan Aubin?

Sojin kasar sun sanar da haka ne a yau Laraba 11 ga watan Oktoba inda su ka umarci jami'ar jin kai ta majalisar da ta dauki dukkan matakan barin kasar.

Kara karanta wannan

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Dira Jihar Arewa, Ya Aike da Kakkausan Saƙo Ga Yan Ta'adda, Ya Ba Su Zaɓi 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jiya Talata 10 ga watan Oktoba ne kasar Faransa ta fara kwashe dakarunta daga kasar da sauran jami'anta cewar Punch.

Wannan na zuwa ne bayan sojin Nijar sun gargadi sojin da su kwashe komatsansu su fice daga kasar.

Sojin Nijar din na zargin Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres da kokarin dakile kasar a babban taron Majalisar da aka gudanar a watan da ya gabata, TRT Afirka ta tattaro.

Wane zargin sojin ke yi kan Majalisar?

Sojin har ila yau, sun soki Sakataren na Majalisar inda su ka ce ya na kokarin kawo cikas a zaman lafiyar kasar.

Bakary Sangare wanda kafin juyin mulkin shi ne jakadan Nijar a Majalisar a yanzu shi ne ministan harkokin wajen kasar.

Har ila yau, shi ne aka zaba don wakiltar kasar yayin taron Majalisar na watan Agusta.

Kara karanta wannan

Hotunan Wike a Gidan Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Na Tsagin Atiku, Bayanai Sun Fito

Rahotanni sun tabbatar da cewa kasar Nijar ta bukaci kasancewa a taron amma ba ta samu dama ba musamman na jerin masu magana a taron.

Nijar ta kori jakadan Faransa a kasar

A wani labarin, Jamhuriyar Nijar ta bai wa Jakadan Faransa, Sylvian Itte wa'adin sa'o'i 48 da ya fice daga kasar.

Sojin na zargin Faransa da munafurtar kasar wurin hada su fada da kungiyar ECOWAS.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.