Isra’ila Ta Yi Alkawarin Kare ’Yan Najeriya Da Ke Kasar Daga Fadawa Rikicin Yaki

Isra’ila Ta Yi Alkawarin Kare ’Yan Najeriya Da Ke Kasar Daga Fadawa Rikicin Yaki

  • Yayin da ake ci gaba da gwabza yaki tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas, ‘yan kasashen waje da ke yankin na cikin tashin hankali
  • Amma jakadan Isra’ila a Najeriya ya yi wa ‘yan kasar da ke yankin cewa babu abin zai same su inda ya ce za a ba su kariya na musamman
  • Michael Freeman ya bayyana haka ne a jiya Talata a Abuja yayIn ganawa da manema labarai kan rikici tsakanin kasashen biyu

FCT, Abuja – Jakadan Isra’ila da ke Najeriya, Michael Freeman ya ce kasar za ta yi duk mai yiyuwa don kare ‘yan Najeriya da ke Isra’ila.

Freeman ya bayyana haka a jiya Talata 10 ga watan Oktoba a Abuja yayin ganawa da ‘yan jaridu, Legit ta tattaro.

Isra'ila ta yi alkawarin kare 'yan Najeriya da ke kasar
Isra’ila Ta Yi Alkawarin Kare ’Yan Najeriay A Kasar. Hoto: Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Twitter

Wane tabbaci Isra'ila ta bai wa Tinubu da 'yan Najeriya?

Kara karanta wannan

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Dira Jihar Arewa, Ya Aike da Kakkausan Saƙo Ga Yan Ta'adda, Ya Ba Su Zaɓi 2

Ya ce hare-haren kungiyar Hamas a Isra’ila ya hallaka dubban mutane wanda shi ne mafi muni tun bayan harin kare dangi a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yakin duniya na biyu da aka shafe tsawon shekaru ana yi tsakanin 1941 zuwa 1945, an kashe dubban Yahudawa.

Jakadan ya ce kungiyar Hamas ta dage wurin karar da ‘yan Isra’ila inda ya sha alwashin cewa sai sun karar da Hamas gaba dayanta a doron kasa.

Wane sako Isra'ila ta tura ga 'yan Najeriya?

Ya tabbatar da ba da tsaro ga ‘yan Najeriya a kasar inda ya ce kowa zai samu kariya amma fa komai na iya faruwa ganin yadda rikicin ke kara kwabewa.

Ya ce:

“Za mu tsare kowa a Isra’ila, ‘yan Najeriya za su samu kariya, za mu yi duk mai yiyuwa don ganin mun kare rasa rayukan mutane a kasar.

Kara karanta wannan

Tinubu Na Shawarar Kirkiro Kotun Musamman Domin Daure Barayin Gwamnati

“Amma tabbas za a rasa rayukan mutane, dole mu shirya wa hakan don ganin mun ba da kariya ga mutane.”

Ku kalli bidiyon Freeman yayin taro da Arise TV ta yada:

Isra’ila ta hallaka Falasdinawa 198 yayin harin ramuwar gayya

A wani labarin, kasar Isra’ila ta kai wani mummunan hari kan Falasdinawa a wani hari na ramuwar gayya da kungiyar Hamas ta yi na makaman roka kan kasar.

A ranar Asabar ce 7 ga watan Oktoba kungiyar Hamas ta kai farmaki kan Isra’ila na bazata wanda ya yi sanadin rayuka da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.