Tinubu Ya Taya Mutanen Libya Alhini Yayin Da Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Kai 6,000
- Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa mutanen Libya bisa ibtila'in ambaliyar ruwan da ya afkawa ƙasar
- Tinubu ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka mutu da fatan samun lafiya ga waɗanda suka jikkata
- Ya ba ƙasar tabbatacin cewa a shirye Najeriya take ta ba su duk gudummawar da suke buƙata
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga ƙasar Libya bisa ibtila'in ambaliyar ruwan da ya janyo sanadin mutuwar mutane aƙalla 6,000.
Wani daga cikin jami'an gwamnatin 'yan aware na ƙasar Libya, Saadeddin Abdul Wakil, ya bayyana cewa aƙalle mutane 6,000 ne aka tabbatar da mutuwarsu a ranar Laraba kamar yadda CNN ta ruwaito.
Mutane da dama sun halaka a ambaliyar ƙasar Libya
Rahotanni sun bayyana cewa dakunan asibitocin da ke yankin sun cika da tarin gawarwakin mutanen da ibtila'in ya shafa, gami da waɗanda suka samu raunuka da ke jiran likitoci su zo su duba su.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An kuma bayyana cewa sama da mutane 30,000 ne suka rasa muhallansu biyo bayan gagarumar ambaliyar ruwan da afku a birnin Derna da garuruwan da ke kewayensa.
Haka nan an kuma bayyana cewa mutane aƙalla 10,000 ne har yanzu ba a gano inda suke ba tun bayan faruwar lamarin.
Tinubu ya aike da sakon taya alhini ga mutanen ƙasar Libya
Shugaba Bola Tinubu ya aike da sakon ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasu a ibtila'in ambaliyar, tare da yin addu'ar Allah ya bai wa waɗanda suka samu raunuka lafiya.
Tinubu ya tabbatarwa da ƙasar ta Libya cewa Najeriya na tare da ƙasar a wannan lokacin na jarabawa da take ciki, kuma a shirye take ta ba da duk gudummawar da ake buƙata.
Ya ƙara da cewa Najeriya tana cikin jimamin abinda ya samu ƙasar na rashin daɗi kamar yadda PM News ta wallafa.
Mutane 15 sun rasu sakamakon haɗarin jirgin ruwa
Legit Hausa a baya ta yi rahoto kan mutane 15 da suka rasa rayukansu sakamakon hadarin jirgin ruwa a jihar Adamawa.
Wani ganau da ya shaida faruwar lamarin ya bayyana cewa wata iska ce ta janyo kifewar jirgin ruwan da yammacin ranar Juma'ar da ta gabata.
Asali: Legit.ng