Rundunar Sojojin Jamhuriyar Nijar Ta Yanke Alakar Soji Da Kasar Benin

Rundunar Sojojin Jamhuriyar Nijar Ta Yanke Alakar Soji Da Kasar Benin

  • Yayin da Jamhuriyar Nijar ke kara shiga matsi daga kasashe, ta fara daukar matakai kan wasu kasashe makwabtanta
  • Sojojin Nijar sun sanar da yanke alakar soji tsakaninsu da Jamhuriyar Benin ganin yadda ta shirya taimakawa kungiyar ECOWAS
  • Wannan na zuwa ne bayan juyin mulki a kasar da sojin su ka kifar da Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin wannan shekara

Yamai, Nijar - Sojojin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun sanar da yanke alakar soji da kasar Benin.

Sojojin sun sanar da haka ne a talabijin na kasar a daren jiya Talata 12 ga watan Satumba na yanke alakar da makwabciyarta Benin.

Sojin Nijar sun yanke alaka da Benin
Rundunar Sojojin Nijar Ta Dauki Mataki Kan Kasar Benin. Hoto: Abdourahmane Tchiani.
Asali: Getty Images

Meye sojin Nijar ke cewa kan Benin?

A cikin wata sanarwa da su ka fitar, sojin su ka ce duk wata yarjejeniya ta kare a tsakaninsu da kasar Benin, cewar PM News.

Kara karanta wannan

An kuma: Sanatan APC ya yi nasara kan PDP a gaban kotu, an yi watsi da duk wani zargi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar kamar ta ce:

"Benin ta ba da umarnin ba da sojoji da na haya da kuma kayan yaki yayin da ECOWAS ke barazanar afkawa Nijar.
"Saboda haka, sojin Nijar sun yanke shawarar yanke alaka da yarjejeniyar soji da Jamhuriyar Benin."

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto Jamhuriyar Benin ba ta yi martani game da wannan mataki na Nijar ba.

Wane takun saka ake tsakanin Nijar da ECOWAS?

Kungiyar ECOWAS na kokarin sulhuntawa da sojin Nijar amma ta tabbatar da daukar matakin soji idan sulhun ya gagara.

Sai dai kungiyar ECOWAS ba ta sanar da yaushe za ta tura dakaru Nijar ba yayin tattaunawar su a makon da ya gabata.

Shugaban kungiyar ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu ya ce za su iya amincewa da dawo da mulkin farar hula cikin watanni tara, cewar Reuters.

Kara karanta wannan

"Ku Yi Hakuri": Sojin Faransa Sun Roki Nijar Karin Lokaci Don Janye Wa A Hankali, Sun Yi Bayani

Sai dai sojin Nijar tun farko sun shirya mika mulki ne a cikin shekaru uku nan gaba.

Nijar Ta Kulla Kawance Na Sojin Burkina Faso Da Mali

A wani labarin, Shugabannin juyin mulkin jamhuriyar Nijar, sun kulla kawance na soji da kasashen Burkina Faso da Mali, wadanda su ma suna karkashin mulkin soji.

Wakilan kasashen uku ne suka fitar da wannan sanarwar ranar Alhamis da ta gabata a Niamey babban birnin kasar.

Wannan na zuwa ne bayan kungiyar ECOWAS na barazanar afka musu da dakaru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.