Sojojin Juyin Mulkin Sun Sanar da Bude Iyakokin Kasar Bayan Rufe Su Na Kwanaki Kadan
- Bayan juyin mulki, kasar Gabon ta sake fitar da sabuwar sanarwa kan matakan da ta dauka a kwanakin bayan nan na rufe iyakokin kasa
- Juyin mulkin Gabon ya jawo cece-kuce, inda ake zargin sojojin wasu kasashen Afrika da maida yankin baya a wannan zamanin
- Kafin Gabon, an yi juyin mulki a kasashen Afrika biyar, lamarin da ke kara dura ruwa a cikin shugabannin nahiyar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kasar Gabon - Sojojin kasar Gabon sun fadi a ranar Asabar cewa za su sake bude iyakokin kasar, wadanda suka rufe sakamakon juyin mulkin da suka yi na hambarar da tsohon shugaban kasar Ali Bongo, Channels Tv ta ruwaito.
Mai magana da yawun shugabannin mulkin sojan Gabon ne ya fadi hakan a gidan talabijin na kasar cewa, sun yanke shawarar ne nan da nan don sake bude iyakokin kasa, ruwa da iska tun daga wannan Asabar din.
Idan baku manta ba, wasu gungun sojojin kasar Gabon su 12 sun sanar a ranar Laraba cewa sun rufe iyakokin kasar har zuwa wani lokacin a wata sanarwar da aka watsa a tashar talabijin ta Gabon 24.
Dalilin yin juyin mulki a Gabon
Janar Brice Oligui Nguema, shugaban rundunar tsaron shugaban kasar a ranar Laraba ne ya jagoranci jami'ansa a juyin mulkin da suka yi wa shugaban kasar Ali Bongo Ondimba, dan gidan da ya shafe shekaru 55 yana mulki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Korar tasa ta zo ne bayan da aka ayyana Bongo mai shekaru 64 a matsayin wanda ya sake lashe zaben shugaban kasa a karshen mako - sakamakon da 'yan adawa suka yi zargin an yi magudi.
Shugabannin juyin mulkin sun ce sun rusa hukumomin kasar tare da soke sakamakon zaben da kuma rufe kan iyakokin kasar, France24 ta ruwaito.
Wasu kasashen da aka yi juyin mulki
Wasu kasashe biyar a Afirka - Mali, Guinea, Sudan, Burkina Faso da Nijar – a yanzu haka suna karkashin shugabannin juyin mulki.
Sabbin shugabannin kasashen biyar sun ki amincewa da bukatar da aka yi musu na komawa bariki cikin kankanin lokaci bayan kwace mulki.
Ana ci gaba da cece-kuce kan yawan juyin mulkin da ake samu a kasashen Afrika cikin shekarun da basu wuce 10 ba yanzu.
Martanin Tinubu ga juyin mulkin Gabon
A bangare guda, shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa abinda yake gujewa bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar, ya tabbata a juyin mulkin da sojoji suka yi wa Ali Bongo na Gabon.
Ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, a lokacin da ya karbi bakuncin Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya, kakashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad Abubakar III.
Tinubu ya bayyana cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun kawo karshen rikicin Nijar ta hanyoyi na diflomasiyya, kafin a kai ga zuwa yaki, wato mataki na karshe da za a iya dauka.
Asali: Legit.ng