Hannayen Jarin Kamfanonin Faransa Sun Fadi Bayan Juyin Mulki A Gabon
- A safiyar yau Laraba aka wayi gari da labarin juyin mulki a kasar Gabon jim kadan bayan sanar da sakamakon zabe
- Dalilin juyin mulkin, kamfanonin Faransa manya-manya guda uku sun gamu da jarrabawar karyewar hannun jari
- Kamfanonin uku sun hada da Maurel/Prom, Eramet, da reshen TotalEnergies da ke kasar Gabon
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Gabon - Bayan kifar da gwamnatin Ali Bongo a kasar Gabon, Faransa ta tafka mummunan asara a kasar.
Rahotanni sun tabbatar cewa hannayen jarin kamfanonin Faransa uku sun fadi a kasuwar hada-hadar hannun jari ta Paris.
Me ya jawo wa Faransa asara a Gabon?
Hakan ya faru ne a yau Laraba 30 ga watan Agusta bayan sojoji sun sanar da kifar da gwamnati a Gabon.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Juyin Mulkin Gabon: Jigon APC Ya Yi Martani Kan Halin Da Ake Ciki, Ya Ce A Saurari Hakan A Wasu Kasashe
Kamfanonin na gudanar da harkokinsu ne a kasar ta Gabon kafin sanar da juyin mulkin, Yeni Safak ta tattaro.
Kamfanonin uku da abin ya shafa sun hada da Maurel/Prom, Eramet, da reshen TotalEnergies na kasar Gabon.
Kamfanonin sun fadi da kashi 15 zuwa 20, a cewar jaridar Faransa ta Les Echos.
Tun farko kamfanin hakar ma'adinai na Eramet ya sanar cewa ya dakatar da ayyukansa da kuma sufurin jiragen kasa a Gabon, cewar TRT Hausa.
Me ke faruwa a Gabon da ya shafi Faransa?
An wayi garin yau Laraba da labarin cewa wasu sojojin Gabon sun sanar a gidan talabijin inda suka yi ikirarin kifar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo
Sanarwar tasu na zuwa ne jim kadan bayan hukumar zaben kasar ta ayyana Shugaba Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben karo na uku.
Ali Bongo ya samu har kashi 64.27 na kuri'un da aka kada a ranar Asabar 26 ga watan Agusta.
Yanzu Yanzu: Bikin Murna Ya Barke a Gabon Yayin da Sojoji Suka Karbe Mulki Daga Shugaban Kasa Ali Bongo, Hotuna Sun Bayyana
Wannan juyin mulki ya kawo karshen shekaru 53 da ahalin gidan Bongo ke rike da madafun ikon kasar.
Ali Bongo ya dare karagar mulki a shekarar 2009 bayan rasuwar mahaifinsa Omar Bongo da ya shafe shekaru da dama a kan karagar mulki.
Sojoji Sun Kifar Da Gwamnatin Bongo A Gabon
A wani labarin, an wayi gari yau da labarin cewa sojojin kasar Gabon sun kifar da Shugaba Ali Bongo.
Wannan na zuwa ne bayan kammala zaben da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
Asali: Legit.ng