Sojojin Nijar Sun Datse Samar Da Wutar Lantarki Da Ruwa Zuwa Ofishin Jakadancin Faransa

Sojojin Nijar Sun Datse Samar Da Wutar Lantarki Da Ruwa Zuwa Ofishin Jakadancin Faransa

  • Yayin da wa’adin sa’o’i 48 da aka bai wa jakadan Faransa a Nijar ya cika, sojin kasar sun sake daukar wasu matakai
  • Sojin sun umarci datse samar da ruwa da kuma wutar lantarki zuwa ofishin jakadancin Faransa da ke Zinder
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa sojin sun gargadi hukumomin da ke da alhakin hakan da su tabbatar sun bi wannan umarni

Yamai, Nijar – Sojojin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar sun umarci katse samar da wuta da kuma ruwa zuwa ofishin jakadancin Faransa da ke kasar.

Sannan sun umarci dakatar da kai abinci zuwa ofishin jakadancin da ke Zinder kamar yadda rahotanni su ka tabbatar a ranar Lahadi 27 ga watan Agusta.

Jamhuriyar Nijar ta datse samar da ruwa da wuta a ofishin jakadancin Faransa
Sojojin Sun Saka Sabbin Takunkumi Ga kasar Faransa A Nijar. Hoto: Legit.ng.
Asali: Facebook

Meye sojin Nijar ke cewa kan Faransa?

Elh Issa Hassoumi, shugaban kwamiti da ke goyon bayan soji (CNSP) shi ya bayyana haka inda ya bukaci dukkan hukumomin da ke samar da ruwa da wuta su guji aikata haka.

Kara karanta wannan

Jan aiki: Sojojin Najeriya sun lalata wata matatun mai da ake aiki ba bisa ka'ida ba

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce duk wata hukuma da aka samu da saba doka, za a dauke ta a matsayin makiyar al’umma a kasar, Anadolu Ajansi ta tattaro.

Wannan na zuwa ne bayan wa’adin da aka bai wa jakadan Faransa na sa’o’i 48 a kasar Nijar ya cika a ranar Lahadi 27 ga watan Agusta.

Wane umarni Nijar ta bai wa jakadan Faransa?

Yayin da ake ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya, Jamhuriyar Nijar ta umarci jakadan Faransa a kasar ya fice tare da ba shi sa’o’i 48.

Idan ba a mantaba, sojin Jamhuriyar Nijar sun kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.

Janar Abdourahamane Tchiani wanda ya kasance tsohon shugaban masu tsaron Bazoum shi ya jagoranci juyin mulkin, TRT Hausa ta tattaro.

Bayan kaddamar da juyin mulkin, kasashe da dama musamman Faransa da wasu kasashen Yammacin duniya su ka soma kwashe ‘yan kasashensu daga Nijar.

Kara karanta wannan

To fah: Kasar Kamaru za ta sako ruwa da madatsa, za a yi ambaliya a Najeriya

Sojin Nijar Sun Kori Jakadan Faransa A Kasar

A wani labarin, sojojin Jamhuriyar Nijar sun kori jakadan Faransa a kasar, Mista Sylvain Itte tare da ba shi sa'o'i 48.

Wannan na zuwa ne bayan kifar da gwamnatin Bazoum da rikicin da ke shirin faruwa tsakanin kasar da sauran kasashen ketare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.