Dan Bindiga Ya Halaka Mutane 3 a Gidan Giya a Kasar Amurka, Ya Raunata Wasu Da Dama

Dan Bindiga Ya Halaka Mutane 3 a Gidan Giya a Kasar Amurka, Ya Raunata Wasu Da Dama

  • Wani ɗan bindiga ya bindige mutane 3 har lahira a harin da ya kai wani gidan giya da ke a jihar California ta Amurka
  • An bayyana cewa dan bindigar, wanda aka tabbatar da cewa tsohon jami'in tsaro ne, ya rasa ransa nan take
  • An alaƙanta harin da rikicin gida tsakanin mutumin da matarsa da ta zo mashayar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

California, Amurka - Aƙalla mutane huɗu ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani hari da wani ɗan bindiga ya kai kan wani fitaccen gidan giya da ke kudancin birnin California.

Jami'an tsaro sun bayyana cewa mutane uku tare da ɗan bindigar ne suka rasa rayukansu a yayin bude wutar da ta faru a gidan giyar kamar yadda BBC ta ruwaito.

Dan bindiga ya sheka mutane 3 s gidan giya
Dan bindiga ya halaka mutane 3 a wata mashayar giya da ke Amurka. Hoto: Crime With Bobby
Asali: Facebook

Yadda ɗan bindiga ya halaka mutane 3 a gidan giya

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Rayuka Da Dama Sun Salwanta Bayan Wani Ginin Bene Ya Rufto a Kan Mutane

Jami'an tsaro sun bayyana cewa, wannan mummunan lamarin ya faru ne ranar Larabar da ta gabata da misalin ƙarfe 7 na yamma.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ɗan bindigar wanda aka bayyana cewa tsohon jami'in tsaro ne, ya buɗe wata kan mai uwa da wabi a yayin da ya isa mashayar giyar.

Mutane uku ne suka mutu nan take, inda aka garzaya da wasu mutanen shida zuwa asibiti domin duba halin da suke ciki.

Dan bindigar ya rasa ransa sakamakon fashewar wani abun fashewa a yayin da suke musayar wuta da jami'an tsaro.

Dalilin da ya sa dan bindiga ya farmaki gidan giyar

An dai alaƙanta farmakin da aka kai a gidan giyar da rikicin gida tsakanin ɗan bindigar da kuma matarsa kamar yadda CBS News ta wallafa.

Sanatan da ke wakiltar yankin mai suna Dave Min, ya bayyana cewa ya kaɗu matuƙa da jin labarin, musamman da ya zamto ana zaman lafiya sosai a yankin na su.

Kara karanta wannan

An Kama Masu Garkuwa Da Mutane 3 Yayin Da Suke Kokarin Karbar Kudin Fansa

Ana dai ci gaba da yawan samun hare-haren 'yan bindiga a sassa daban-daban na ƙasar Amurka, wanda hakan ya sa 'yan ƙasar da dama ke ganin ya kamata a ɗauki tsauraran matakai kan mallakarta.

Mayaƙan Boko Haram da ISWAP 41 sun halaka a sabon rikici

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wani ƙazamin rikici da ya ɓarke a tsakanin mayaƙan 'yan ta'adda na ƙungiyar Boko Haram da kuma na ISWAP.

Mayaƙa aƙalla 41 ne, ciki kuwa har da manyan kwamandojinsu aka tabbatar da sun mutu a yayin artabu tsakanin ƙungiyoyin biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng