Nijar: Algeria Da Egypt Sun Ki Amincewa Da Amfani Da Matakin Soji a Kan Sojojin Juyin Mulki

Nijar: Algeria Da Egypt Sun Ki Amincewa Da Amfani Da Matakin Soji a Kan Sojojin Juyin Mulki

  • Ƙasashen Algeria da Egypt, sun nuna rashin amincewarsu kan amfani da ƙarfin soji a Nijar
  • Ƙasashen sun ce zama a kan teburin tattaunawa shi ne abinda ya fi dacewa wajen warware rikicin
  • Yanzu haka ƙasashen na kan tuntubar ECOWAS domin ganin sun hana faruwar yaƙin da ke shirin ɓarkewa

Ƙasashen Algeria da Egypt, sun nuna kin amincewarsu kan amfani da ƙarfin soji wajen shawo kan rikicin siyasar jamhuriyar Nijar, sun ce tattaunawa ce ainihin abinda ya dace a yi.

Hakan dai yana zuwa ne a lokacin da ƙungiyar ECOWAS ta nuna alamomin cewa za ta iya yin amfani da ƙarfin soji wajen dawo da dimokuraɗiyya a Nijar.

Algeria da Egypt ba su amince a yi amfani da ƙarfin soji a Nijar ba
Algeria da Egypt sun ce amfani da ƙarfin soji a Nijar zai iya jefa Afrika cikin rikici. Hoto: RTN-EFE
Asali: Getty Images

Algeria ta nemi a bi matakai na diflomasiyya

Domin shawo kan rikicin na Nijar, shugaban Algeria Abdelmadjid Tebboune, ya tashi ministan harkokin wajen ƙasar Ahmed Attaf, zuwa Najeriya, Benin da Ghana.

Kara karanta wannan

Aljeriya Na Ba Nijar Wutar Lantarki Kyauta Bayan Najeriya Ta Dai Na Ba Su? Gaskiya Ta Bayyana

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Attaf zai gana da wakilan ECOWAS na waɗannan ƙasashe domin ganin an warware rikicin ta hanyar diflomasiyya ba ta amfani da ƙarfin soji ba kamar yadda Africa News ta ruwaito.

A baya shugaban ƙasar na Algeria ya yi gargaɗin cewa amfani da karfin soji a Nijar zai janyo yaƙin da zai shafi ƙasarsa wacce ta haɗa iyaka da mai tsawon kilomita 1,000 da Nijar.

Egypt ta bukaci a tattauna domin shawo kan rikicin

A na ta ɓangaren, gwamnatin ƙasar Masar (Egypt), ta muhimmantar da cewa bin matakai na tattaunawa wajen shawo kan rikicin siyasar Nijar shi ne abinda ya fi kamata a yi.

Ta ce yin amfani da ƙarfin soji kan rikicin zai iya janyo fitinar da za ta addabi ƙasashen Afrika ta Yamma da ma sauran ƙasashen Afrika baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Abdourahmane Tchiani Ya Fadi Matakin Da Za Su Dauka Idan ECOWAS Ta Kawowa Nijar Hari

Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta Masar, ta ce tana yin iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta hana faruwar rikicin da ka iya shafar tsaro da zaman lafiyar yankin gaba ɗaya.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sama da 'yan gudun hijira sama da 7,000 da ke tsallakawa zuwa wasu ƙasashen suka maƙale a Nijar kamar yadda VOA News ta wallafa.

Sojojin Nijar ba za su mayar da Bazoum kan mulki ba

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan jawabin da sojojin juyin mulkin jamhuriyar Nijar suka yi a yayin ganawarsu da tawagar ECOWAS da Abdulsalami Abubakar ya jagoranta.

Sun ce a shirye suke su tattauna kowane abu da ake buƙata, amma banda batun mayarwa da Bazoum kujerarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng