Janar Tchiani Ya Soki Kungiyar ECOWAS Kan Takunkunmin Da Ta Sanyawa Nijar

Janar Tchiani Ya Soki Kungiyar ECOWAS Kan Takunkunmin Da Ta Sanyawa Nijar

  • Shugaban gwamnatin sojojin Jamhuriyar Nijar ya sake fitar da sabon bayani ta gidan talabijin na ƙasar
  • Janar Abdourahamane Tchiani ya soki takunkumin da ƙungiyar ECOWAS ta ƙaƙaba wa ƙasar
  • Shugaban ya buƙaci ƙungiyar ta ɗage takunkumin da ta sanya kan ƙasar saboda yadda yake wahalar da al'ummar Nijar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jamhuriyar Nijar - Shugaban gwamnatin sojojin Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya soki takunkumin da ƙungiyar ECOWAS ta ƙaƙaba wa ƙasar, inda ya ce babu adalci a ciki.

Shugaban gwamnatin ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabi da ya yi a gidan talabijin ranar Asabar da daddare, rahoton Aljazeera ya tabbatar.

Tchiani ya caccaki kungiyar ECOWAS
Janar Tchiani ya soki takunkumin da ECOWAS ta sanyawa Nijar Hoto: RTN-EFE
Asali: Getty Images

Tchiani ya yi jawabin ne bayan ya gana da tawagar ƙungiyar ECOWAS, a ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayanai Sun Fito Yayin Da Tawagar Abdulsalami Ta Kasa Haduwa Da Janar Tchiani

Shugaban ya buƙaci a gwamnatin tarayyar Najeriya da ta mayar da wutar lantarkin da ta yanke wa ƙasar, wanda hakan yana daga cikin takunkumin da a ka ƙaƙaba kan sojojin juyin mulkin bayan sun hamɓarar da Shugaba Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya soki takunkumin ECOWAS

Ya bayyana cewa takunkumin na ECOWAS ba su kamata ba, inda ya ƙara da cewa an sanya su ne kawai da nufin wahalar da mutanen Nijar, cewar rahoton Daily Trust.

A cewarsa yara da sauran marasa lafiya na rasuwa a asibitoci saboda rashin wutar lantarki.

Ya bayyana cewa kulle iyakokin da aka yi ya sanya samun abinci, magani da sauran abubuwan amfani na yau da kullum ya zama abu mai matuƙar wahala.

Tchiani ya ce ECOWAS na shirin afkawa Nijar

A cikin jawabin da ya yi na mintuna 12, Tchiani ya yi iƙirarin cewa ECOWAS tana shirin kai farmaki kan Nijar ta hanyar kafa runduna tare da yin haɗaka da sojojin ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

An Shiga Tashin Hankali Bayan Burkina Faso Da Mali Sun Aike Da Jiragen Yaki Zuwa Jamhuriyar Nijar

"Ina ƙara tabbatar da cewa ƙwace mulki ba shi ba ne burinmu. Ina ƙara tabbatar da shirinmu na hawa kan teburin sulhu inda har ya yi duba kan abubuwan da al'ummar Nijar su ke so." A cewarsa.

Tchiani Zai Shekara Uku a Kan Mulki

A wani labarin kuma, shugaban gwamnatin sojojin Nijar ya bayyana shekarun da za su yi akan mulki kafin su miƙa wa farar hula.

Janar Abdourahamane Tchiani ya bayyana cewa sai sojoji sun yi shekara uku akan mulki kafin su sauka daga kan madafun iko a Nijar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng