Tawagar ECOWAS Ba Ta Samu Damar Tattaunawa Da Janar Tchiani Ba
- Tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, ya jagoranci tawagar ECOWAS domin tattaunawa da sojojin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar
- Sai dai, tawagar ba ta samu tatttaunawa da shugaban gwamnatin sojin ba, a maimakon hakan sai ta gana da Firaminista Ali Lamine Zeine
- An shiga halin rashin tabbas kan dalilin rashin tattaunawa da shugaban inda wasu rahotanni ke cewa dakarun tsaron shugaban ƙasar ne suka yi bore
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jamhuriyar Nijar - Tawagar ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) a ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar, ta sake komawa Jamhuriyar Nijar.
Tawagar ta ECOWAS ta sake komawa Nijar ne domin tattaunawa da sojojin juyin mulkin Nijar, kan yadda za a warware rikicin cikin ruwan sanyi.
Gwamnatin sojojin ta Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da zuwan tawagar wakilan na ECOWAS, cewar rahoton Aljazeera.
Tawagar ECOWAS ta gana da Ali Zeine
Duk da cewa tawagar an shirya za su gana da shugaban gwamnatin sojojin, Janar Abdourahamane Tchiani, Firaministan ƙasar, Ali Lamine Zeine shi ne ya tarbe su.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar rahoton Daily Trust wanda ta samo daga BBC Hausa, zaman tattaunawar da wakilan na ECOWAS suka yi ya shafe kusan mintuna 90.
Ba a san ainihin takamaiman dalilin da ga sanya tawagar Abdulsalami ba ta gana da Janar Tchiani ba, amma wasu rahotannin da ba a tabbatar da su ba, sun nuna dakarun tsaron shugaban ƙasar sun yi bore ne.
Tawagar farko wacce Abdulsalami ya jagoranta a baya, ba ta samu ganin Shugaba Bazoum ba da shugaban gwamnatin sojojin, Janar Tchiani
Daga baya Tchiani ya bayar da haƙuri kan rashin sauraron tawagar lokacin da wasu malaman addinin musulunci daga Najeriya suka ziyarce shi, inda ya ce sun ƙi sauraron tawagar ne saboda fushin da suka yi kan takunkumin da ECOWAS ta ƙaƙabawa ƙasar.
Yanzu: A Shirye Mu Ke Mu Kai Hari Nijar, Dakarun ECOWAS Sun Yi Bayani Bayan Taronsu Na Ranar Alhamis
AnAike Da Jiragen Yaki Zuwa Nijar
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙasashen Mali da.Burkina Faso sun aike da jiragen yaƙinsu ziwa Jamhuriyar Nijar.
Ƙasashen biyu sun aike da jiragen yaƙin ne domin taimaka wa ƙasar bisa barazanar yaƙin da ƙungiyar ECOWAS ke shirin ƙaddamar wa a kan ƙasar.
Asali: Legit.ng