Kasashen Mali Da Burkina Sun Aika Da Jirage Yaki Zuwa Jamhuriyar Nijar

Kasashen Mali Da Burkina Sun Aika Da Jirage Yaki Zuwa Jamhuriyar Nijar

  • Gwamnatocin sojojin ƙasashen Burkina Faso da Mali sun aike da jirage yaƙi zuwa Jamhuriyar Nijar
  • Gwamnatocin sun aike da jiragen ne domin taimaka wa Nijar ta kare kanta kan barazanar yaƙin da ECOWAS ke yi
  • An tura jiragen yaƙin ne yayin da Nijar ta fara ɗaukar sojojin sa-kai da za su taimaka mata fafata yaƙi da ECOWAS idan akwai buƙatar hakan

Jamhuriyar Nijar - Gwamnatocin sojojin ƙasashen Burkina Faso da Mali sun cika alƙawarin da suka ɗauka na taimaka wa Jamhuriyar Nijar wajen daƙile barazanar yin amfani da ƙarfin soja da ECOWAS ke yi.

Gwamnatocin ƙasashen biyu sun aike da jiragen yaƙi ɗai-ɗai domin taimaka wa Jamhuriyar Nijar ta yaƙi matakin yin amfani da ƙarfin soja da ƙungiyar ECOWAS ke shirye-shiryen ɗauka a ƙasar.

Burkina Faso da Mali sun tura jiragen yaki zuwa Nijar
Kasashen Mali da Burkina Faso sun aika jiragen yaki zuwa Nijar Hoto: Airsourcemilitary.com
Asali: UGC

Jaridar Aminiya ta rahoto cewa gidan talabijin na gwamnatin Nijar ya bayyana cewa Burkina Faso da Mali, sun ajiye jiragen ƴaƙinsu a kan iyakokin Jamhuriyar Nijar a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Yanzu: A Shirye Mu Ke Mu Kai Hari Nijar, Dakarun ECOWAS Sun Yi Bayani Bayan Taronsu Na Ranar Alhamis

Rahoton ya bayyana cewa gwamnatin sojojin ta Nijar ta yaba da haɗin kan da ƙasashen biyu su ke ba ta, da cewa sun bayyana a aikace wajen cika alƙawarin da suka ɗauka bisa ajiye jiragen yaƙinsu domin ragargazar masu shirin kai hari a Nijar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An fara dauƙar sojojin sa-kai a Nijar

Gwamnatin sojin Nijar za ta fara ɗaukar sojojin sa-kai a ranar Asabar, a shirinta na fafatawa da dakarun ƙungiyar ECOWAS, waɗanda ke shirin yin amfani da ƙarfin soja wajen tabbatar da dawo da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar.

Matasa waɗanda ba su gaza shekara 18 a duniya ba ne za a ɗauka a rundunar sa-kan wacce aka sanya wa sunan VDN a takaice.

Za a tantance matasan ne a filin wasa na Janar Seyni Kountche, wanda yake a birnin Yamai. Sannan za a tantance wasu matasan a iyakokin ƙasar na Jamhuriyar Benin da Najeriya.

Kara karanta wannan

Abinda Sakataren Amurka Ya Faɗawa Tinubu Kan ECOWAS Dangane Da Juyin Mulkin Nijar

Aikin da mayaƙan sa-kan za su yi

Mayaƙan na sa-kai za su riƙa taimaka wa sojojin Nijar a filin yaƙi, sufuri da kula da lafiya da ire-irensu idan har akwai buƙatar hakan.

Ƙasar Burkina Faso ita ma tana da irin wannan rundunar ta sa-kai, wacce ta kafa domin yaƙi da ta'addancin da take fama da shi a ƙasar.

Tinubu Ya Gargadi Sojojin Juyin Mulkin Nijar

A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gargaɗi sojojin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar.

Bola Tinubu ya gargaɗi sojojin ne kan lafiyar Shugaba Bazoum, inda ya ja kunnensu kan kada su kuskura lafiyar hamɓararren shugaban ta taɓarɓare a hannunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng