Dattijuwa Mai Shekara 110 a Duniya Ta Koma Makaranta a Saudiyya
- Wata tsohuwa mai shekara 110 ta ƙudiri aniyar yaƙi da jahici bayan ta koma makaranta domin samun ilmi
- Dattijuwar ta koma makarantar ne bayan ta daɗe tana da burin yin karatu amma ba ta samu damar hakan ba
- Nawda Al-Qahtani mai ƴaya huɗu a duniya ta samu ƙarfawa gwiwa daga wajen ƴaƴanta waɗanda suka yi na'am da hukuncin da ta yanke
Kasar Saudiyya - Wata tsohuwa mai shekara 110 a duniya ƴar ƙasar Saudiyya, mai suna Nawda Al-Qahtani, ta koma makaranta domin samun ilmi.
Nawda Al-Qahtani dai ta yanke shawarar komawa aji ta samu karatu ne domin ta yi yaƙi da jahilci, rahoton Saudi Moments ya tabbatar.
Dattijuwar wacce take da ƴaƴa huɗu, waɗanda babbansu yake da shekara 80 sannan ɗan autan yana da shekara 50, ta bayyana cewa ba ta taɓa ɓacin rai ba tun da ta fara zuwa makarantar.
Dattijuwar ba ta wasa da duk wani aikin gida da malamai ke bayar wa a makaranta, inda ita da sauran takwarorinta masu manyan shekaru su ke koyon karatun Al-Kur'ani da haɗa baƙi, cewar rahoton Arab News.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Makarantar mai suna Al-Rahwa da ke a yankin Umwah, tana da ɗalibai masu kowane irin shekaru masu halartar ta.
Ta daɗe tana son shiga makaranta
Malama Nawda ta bayyana cewa ta daɗe tana son shiga makaranta, amma ba ta samu damar hakan ba, sai yanzu da ta jajirce ta aikata hakan.
Ta alaƙanta rashin komawa makaranta da ba ta yi ba a baya, kan yanayin yankunansu na ƙauyuka inda ƴaƴa mata ba su samun dama su kammala karatu.
Dattijuwar ta yaba wa gwamnatin Saudiyya bisa ƙoƙarin da take na kawar da jahilci a ƙasar, inda ta ce da a ce ta daɗe da komawa makaranta, da tana da tabbacin hakan ya inganta mata rayuwa da ta sauran mutane masu shekaru irin na ta.
Tashin Hankali Yayin Da Barayi Suka Banka Wa Shagunan 'Yan Kasuwa Wuta Bayan Tafka Sata a Jihar Arewa
Ƴaƴanta na goyon bayan komawar da ta yi zuwa makaranta, inda su ke ci gaba da ƙarfafa mata gwiwa da yi mata kyakkyawan fata.
Ƴaƴan dattijuwar sun bayyana rashin komawarta a makaranta a matsayin wata ƙaddara daga Allah.
Yara Masu Tafiya Daga Kamaru Zuwa Najeriya Neman Ilmi
A wani labarin kuma, bidiyom wasu yara masu tafiya a ƙafafunsu daga Kamaru zuwa Najeriya neman ilmi ya ɗauki hankula.
Bidiyon yaran masu yin wannan doguwar tafiyar dai ya tsuma zukatan masu amfani da yanar gizo.
Asali: Legit.ng