Juyin Mulkin Nijar: ECOWAS Ta Yi Sabon Jawabi Kan Halin Da Bazoum Da Dansa Ke Ciki a Tsare

Juyin Mulkin Nijar: ECOWAS Ta Yi Sabon Jawabi Kan Halin Da Bazoum Da Dansa Ke Ciki a Tsare

  • ECOWAS ta ce hambararren shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum yana rayuwa cikin mugun yanayi kuma dansa ya zabge sosai
  • Kungiyar ta yammacin Afrika ta ce Bazoum da iyalinsa na tsare a cikin yanayi na rashin imani
  • Kungiyar ta gargadi Janar Abdourahmane Tchiani da ya janye daga aiwatar da barazanarsa na kashe Bazoum

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta yi karin haske kan yanayin da hambararren shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum da dansa suke ciki.

Kwamishinan ECOWAS kan harkokin siysa, zaman lafiya da tsaro, Ambasada Abdel-Fatau Musah, ya ce Bazoum da dansa suna cikin mugun yanayi a tsare a hannun masu juyin mulki.

Bazoum na cikin mugun yanayi a hannun masu juyin mulki
Juyin Mulkin Nijar: ECOWAS Ta Yi Sabon Jawabi Kan Halin Da Bazoum Da Dansa Ke Ciki a Tsare Hoto: Nigerian Presidency/@realFFK
Asali: Twitter

Bazoum na cikin mugun yanayi, dansa ya zabge sosai

Musah ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a shirin Channels TV na Sunrise Daily a ranar Juma'a, 11 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Sojojin Juyin Mulki Za Su ‘Kashe’ Bazoum Idan Dakarun ECOWAS Suka Duro Nijar

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Za mu je chan, idan bukatar haka ta taso, don ceto Shugaba Bazoum wanda ke rayuwa a wani mugun yanayi a yau. An hana shi samun kulawar likitoci, an hana shi samun abincin da ya saba da shi.
"Dansa wanda shina yana tsare, ya zabge inda ya rasa kilo masu yawa zuwa yanzu. Ana tsare da su a yanayi na rashin imani kuma ba za mu zaune ba tare da yin wani abu ba da dogaro da nufin wadannan mutane wadanda ke hargitsa tarin damokradiyya a kasar."

Da yake martani kan barazanar da shugaban mulkin soja, Janar Abdourahmane Tchiani ya yi na kashe Bazoum, idan kungiyar ECOWAS ta aiwatar da shirinta na daukar matakin amfani da sojoji a kan Jamhuriyar Nijar, Musah ya ce masu juyin mulkin za su biya bashi idan suka illata Bazoum da iyalinsa.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Asari Dokubo Ya Sha Alwashin Yin Kasa-Kasa Da Gwamnatin Sojan Nijar

Rahoton ya kuma nakalto yana cewa:

"Sanarwar jiya ta kuma bayyana karara cewa wannan gwamnati na mulki soji za ta biya bashi idan wani abu ya faru da kariuya, tsaro ko lafiyar Bazoum da iyalinsa ko mambobin gwamnatinsa. A bayyane aka yi wannan."
“Ba za mu ja da baya ba saboda suna rike da shugaban kasar. Idan suka kuskura, idan har za su cutar da su ta kowace hanya, to za su biya bashi sosai a kan hakan. Don haka wannan dabara ce.”

Sarkin Musulmi bai yarda da matakin ECOWAS kan Nijar ba

A wani labarin, mun ji a baya cewa majalisar Koli ta harkokin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta bayyana matsayinta dangane da takunkumin da kungiyar kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta kakaba ma jamhuriyar Nijar.

A ranar Laraba, 9 ga watan Agusta, mataimakin babban sakataren NSCIA, Salisu Shehu, ya ce majalisar ta yi adawa da takunkumin da ECOWAS ta kakabawa Nijar sakamakon juyin mulkin da aka yi a ranar 26 ga watan Yuli a kasar ta yammacin Afrika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel