Amurka Ta Gargadi Sojojin Nijar Kan Taba Lafiyar Bazoum, Ta Goyi Bayan ECOWAS
- Kasar Amurka ta yi magana dangane da halin da ake ciki a jamhuriyar Nijar
- Ta gargaɗi sojojin juyin mulkin na Nijar kan taɓa lafiyar Bazoum da kuma iyalansa
- Haka nan ƙasar ta Amurka ta goyi bayan ƙoƙarin da ƙungiyar ECOWAS take yi na ganin an dawo da dimokuraɗiyya a Nijar
Kasar Amurka ta ce ta ɗora alhakin kare lafiyar hamɓararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum, iyalansa da kuma mambobin majalisar ministocinsa da ake tsare da su a hannun sojojin ƙasar.
Ta buƙaci kada sojojin da suka yi juyin mulkin su cutar da Bazoum ko wani daga cikin ahlinsa kamar yadda PM News ta ruwaito.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen ta Amurka ta fitar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amurka ta nemi a dawo da mulkin dimokuraɗiyya a Nijar
Blinken ya bayyana cewa Amurka na goyon bayan ƙoƙarin da ECOWAS take yi na ganin an dawo da mulkin dimokuradiyya a jamhuriyar Nijar.
Sai dai jawabin na sa bai goyi bayan matakin amfani da ƙarfin soji da mambobin ƙasashen na ECOWAS suke shirin yi ba.
Amurka ta ba da shawarar cewa amfani da ƙarfin soji ya zamo abu na ƙarshe da ECOWAS za ta yi in duk matakan diflomasiyya ba su yi tasiri ba.
ECOWAS ta bai wa sojojinta umarnin ɗaura ɗamarar yaƙi
A rahoton Legit.ng na baya, kungiyar ECOWAS ta umarci dakarunta da su ɗaura ɗamarar yaƙi, su kasance cikin shirin ko ta kwana domin tunkarar sojojin Nijar da suka yi juyin mulki.
Matakin na zuwa ne bayan tsallake wa'adin da ECOWAS ta bai wa sojojin jamhuriyar Nijar na su .ayar da mulki ga hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.
A ranar 26 ga watan Yuli ne dai shugaban dakarun da ke bai wa shugaban ƙasa tsaro, Janar Abdourahmane Tchiani, ya jagoranci hamɓarar da gwamnatin Bazoum.
Hakan ya janyo suka da Allah wadai daga ƙungiyoyi da sassa daban-daban na duniya.
Matakan ECOWAS 4 da suka janyo barazana ga rayuwar Bazoum
Legit.ng a baya ta haɗa wani rahoto kan abubuwa hudu da ake ganin sune suka ƙara ingiza sojojin juyin mulkin Nijar wajen yin barazana ga rayuwar Mohamed Bazoum.
A ranar Alhamis ne dai aka samu labarin cewa sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar, sun sha alwashin halaka shi idan ECOWAS ta afka mu su da yaƙi.
Asali: Legit.ng