Tinubu Da Wasu Shugabanni 7 Sun Fara Taron ECOWAS Kan Juyin Mulkin Nijar
- Shugaban kasa Bola Tinubu da wasu shugabanni bakwai na kungiyar ECOWAS sun fara taro na musamman kan rikicin Jamhuriyar Nijar a Abuja
- Sauran shugabanni biyu, Faure Essozimna Gnassingbé Eyadéma na Togo da shugaban Adama Barrow na kasar Gambiya suna kan hanya
- Taron na ECOWAS na zuwa ne bayan gwamnatin sojan Nijar sun ki bin wa’adin da ta basu na mika mulki ga gwamnatin damokradiyya
Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya jagoranci sauran shugabannin kasashen yammacin Afrika zuwa wani babban taron Kungiyar Raya Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) kan rikicin siyasar Jamhuriyar Nijar, rahoton Daily Trust.
Ku tuna cewa shugaban kasa Tinubu, shugaban kungiyar ECOWAS, ya shirya wani taro bayan wa'adin da aka diba ma shugabannin mulkin sojan Nijar na mayar da Shugaban kasa Mohamed Bazoum ya cika.
Dalilin da yasa shugaban kasa Tinubu da sauran shugabannin ECOWAS suka taro na musamman
Bazoum ne zababben shugaban kasar Nijar na damokradiyya, amma masu juyin mulkin sun yi watsi da kungiyar kasashen yankin, lamarin da ya sa aka kara sanyawa magoya bayan sojojin takunkumi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kungiyar ECOWAS dai ta yi karin haske kan yiwuwar daukar matakin amfani da sojoji a kan gwamnatin mulkin soja, wanda mutane da dama musamman yan Najeriya suka nuna adawa da hakan.
Yayin da aka dakatar da mambobin kungiyar ECOWAS biyar saboda juyin mulkin soja, taron na musamman ya fara da mambobin kungiyar takwas. Haka kuma, biyu basu hallara ba tukuna, rahoton Punch.
Jerin shugabannin da suka halarci taron
- Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio
- Shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Mokhtar Sissoco
- Shugaban kasar Burundi Everiste Ndayishimiye
- Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara
- Shugaban kasar Mauritania Mohamed Ould Ghazouani
- Shugaban kasar Ghana Nana Akofo-Ado
- Shugaban kasar Senegal Macky Sall
- Shugaban Jamhuriyar Benin Patrice Talon
Wadanda basu hallara ba
- Togo. Faure Essozimna Gnassingbé Eyadéma
- Shugaba Adama Barrow na Gambiya
Meye Asari yake shirin yi ga sojin Nijar?
A wani labarin, tsohon shugaban kungiyar tsagerun Niger Delta, Asari Dokubo, ya bugi kirjin cewa zai yi kasa-kasa da masu juyin mulki a Nijar da dakarunsu idan har gwamnatin tarayya da kungiyar ECOWAS suka daura masa alhakin yin haka.
Dokubo wanda ya kasance mutum mara tsoro ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya yadu kuma Legit.ng ta gani a ranar Alhamis, 10 ga watan Agusta.
Asali: Legit.ng