ECOWAS Ta Sake Sanya Sabbin Takunkumi Kan Juyin Mulkin Jamhuriyar Nijar

ECOWAS Ta Sake Sanya Sabbin Takunkumi Kan Juyin Mulkin Jamhuriyar Nijar

  • Ƙungiyar ECOWAS, a ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta sake ƙaƙaba takunkumi kan magoya bayan sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
  • Ajuri Ngelale, kakakin shugaban ƙasa Bola Tinubu, shi ne ya bayyana hakan a ranar Talata inda ya ce za a ƙaƙaba takunkumin ne ta hannun CBN
  • Kakakin shugaban ƙasar bai yi cikakken bayanin yadsa takunkumin zai yi aiki ba, amma kalamansa na zuwa ne a daidai lokacin da wa'adin da aka ba sojojin ya ƙare

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) ta sake sanya sabbin takunkumi kan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar.

Ƙungiyar ta ECOWAS tun da farko ta ba sojojin da suka yi juyi mulki a ƙasar wa'adin kwana bakwai na su mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan muƙaminsa, ko ta ƙaƙaba musu takunkumi ciki har da amfani da ƙarfin soja.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Sake Sanya Labule Da Farfesa Okonjo-Iweala, Bayanai Sun Bayyana

ECOWAS ta sake sanya sabbin takunkumi kan Nijar
ECOWAS ta sake kakaba sabbin takunkumi kan Nijar Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Amma sojojin da suka yi juyin mulkin sun yi biris da barazanar ECOWAS sannan suka sha alwashin daƙile duk wani shiga tsakani daga ƙasar waje da za ayi a Nijar.

Biyo bayan hamɓarar da gwamnatin dimokuraɗiyya da sojojin suka yi, sojojin da suka yi juyin mulkin sun kuma datse dangantakar diflomasiyya da Najeriya, Faransa, Amurka da Togo sannan suka. kulle sararin samaniyar ƙasar har sai abin da hali ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane takunkumi ECOWAS ta sake sanya wa?

Da yake tattaunawa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa a ranar Talata 8 ga watan Agusta, kakakin shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya bayyana cewa an ƙara sanya takunkumi akan masu hulɗa da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Duk da dai bai yi cikakken bayani ba, ya bayyana cewa an yi hakan ne ta hannun babban bankin Najeriya (CBN).

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: ECOWAS Ta Sanar Da Ranar Da Za Ta Sake Zama Don Yanke Hukunci Kan Nijar

Abubuwan Da Suka Faru a Juyin Mulkin Nijar

A wani labarin na daban kuma, mun tattaro mu ku abubuwa muhimmai da suka faru dangane da juyin mulkin Jamhuriyar Nijar.

Tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Shugaba Bazoum dai abubuwa sun faru masu yawa a Nijar ciki har da wa'adin da ECOWAS ta bayar da biris ɗin da sojoji suka yi kan wa'adin n ECOWAS.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng