Juyin Mulkin Nijar: Shugabannin ECOWAS Sun Gana Bayan Wa'adin Da Suka Bayar Ya Cika
- Shugabannin ƙungiyar raya tattalin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) sun gana kan matsalar juyin mulkin Nijar
- Shugabannin sun gana ne bayan wa'adin sati ɗaya da suka ba Janar Tchiani na sauka daga kan mulki ya cika
- A yayin taron na su sun cimma matsayar sake gudanar da wani taron domin ɗaukar matakin ƙarshe kan sojojin juyin mulkin Nijar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Shugabannin ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) da ƙungiyar tarayyar Afirika (AU) sun yi taron gaggawa a ranar Lahadi, 6 ga watan Agusta.
Shugabannin sun gudanar da taron ne domin tattaunawa kan mataki na gaba da za su ɗauka bayan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar.
Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, taron gaggawar an gudanar da shi ne bayan wa'adin miƙa wuya da da ƙungiyar ECOWAS ta ba sojojin juyin mulkin ya ƙare a jiya Lahadi.
Juyin Mulki: Sojojin Nijar Sun Kulle Sararin Samaniyar Kasar Yayin Da ECOWAS Ke Barazanar Amfani Da Karfin Soja
An tattaro cewa ƙungiyar ECOWAS za ta sake shirya wani taron a cikin kwanaki masu zuwa domin cimma matsaya kan matakin da za su ɗauka na gaba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jaridar The Punch ta rahoto wata majiya a fadar shugaban ƙasa a Abuja ta bayyana cewa:
"Shugabannin za su sake zama domin cimma matsaya kan mataki na gaba da za su ɗauka. Amma ba a sanya ranar da za a sake yin taron ba inda za a ɗauki matakin ƙarshe kan yadda za a magance matsalar dake faruwa a Jamhuriyar Nijar."
Daga cikin mahalarta taron akwai gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, gwamnan jihar Kebbi, Idris Nasir da gwamnan jihar Katsina Dr Dikko Umar Radda.
Yunƙurin sasantawa na ECOWAS bai haifar da ɗa mai ido ba
A halin da ake ciki, ƙungiyar ECOWAS ta yi ƙoƙarin cimma matsaya cikin ruwan sanyi da Janar Tchiani domin tattauna yadda za a saki Shugaba Mohamed Bazoum, wanda yake a tsare tun ranar Laraba, 26 ga watan Yuli lokacin da sojoji suka kifar da gwamnatinsa.
Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Abdulsalam Abubakar da Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III da wasu dattijan ECOWAS an tura su a matsayin wakilai zuwa Nijar domin cimma matsaya kan zaman lafiya
Sai dai, duk da hakan Janar Tchiani ya ƙi yarda a hau kan teburin sulhu da shi.
Sojojin Nijar Sun Kulle Sararin Samaniyar Kasar
A wani labarin kuma, sojojin da suka gudanar da juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun kulle sararin samaniyar ƙasar.
Janar Abdourahamane Tchiani shi ne ya bayar da wannan umarnin kan fargabar afka musu da ECOWAS za ta iya yi, bayan wa'adin sati ɗaya da ta bayar ya cika.
Asali: Legit.ng