Janar Tchiani: Abubuwan Sani Dangane Da Sojan Da Kitsa Juyin Mulki a Jamhuriyar Nijar

Janar Tchiani: Abubuwan Sani Dangane Da Sojan Da Kitsa Juyin Mulki a Jamhuriyar Nijar

Hamɓarar da gwamnatin farar hula da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar ranar Laraba, 26 ga watan Yuli, ya kasance juyin mulki na kwana-kwanan nan da aka yi tun na Ƙasar Mali a shekarar 2021.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani muhimmin abu dangane da waɗannan juyin mulkin shi ne duk sun faru ne a yankin Afirika ta Yamma, wanda hakan yake kawo shakku cewa mulkin dimokuraɗiyya bai samun tagomashi a yankin.

Abubuwan sani dangane da Janar Tchiani
Janar Tchiani sojan da ya kifar da gwamnati a Nijar Hoto: ORTN - Télé Sahel/AFP Hoto
Asali: Getty Images

Janar Abdourahamane Tchiani, shugaban dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa a Jamhuriyar Nijar, tare da dakarun ƴan tawayensa, sun cafke Shugaba Bazoum tare da hamɓarar da gwamnatinsa.

Ga wasu muhimman abubuwan sani dangane da Janar Tchiani

1. Aikin Janar Tchiani a gidan soja

Janar Abdourahamane Tchiani shi ne shugaban dakarun tsaron Shugaban ƙasa Mohamed Bazoum, wanda ya kifar da gwamnatinsa, bisa bayar da dalilan cin hanci da rashin gaskiya na mai gidansa.

Kara karanta wannan

Ta Fasu: An Faɗi Sunan Wanda NEC Ke Shirin Naɗa Wa a Matsayin Shugaban APC Na Ƙasa Ranar Alhamis

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A shekara 59 a duniya, Janar Tchiani shi ne soja mafi girma a tarihin Jamhuriyar Nijar, inda ya yi aiki a ƙarƙashin shugabannin ƙasa guda biyu.

Aikinsa na farko a matsayin babban soja ya yi shi ne a ƙarƙashin tsohon shugaban ƙasa Mahamadou Issoufou, sannan sai a ƙarƙashin Shugaba Bazoum.

2. Shahararsa

Saboda nasarorin da ya samu a aikin soja, Janar Tchiani sananne a wajen al'ummar ƙasar insa ake girmama shi saboda ƙarfin ikon soja da yake da shi.

Ibrahim Yahaya Ibrahim, wani mai bincike na ƙungiyar 'International Crisis Group think tank', ya bayyana cewa :

"Ba sananne ba ne sosai idan ba a gidan soja ba. Mutum ne wanda yake a ɓoye mai ƙarfin iko."

3. Rigimarsa da Shugaba Bazoum

A ranar Juma'a, Tchiani ya ayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa bayan ya kitsa juyin mulki wanda ya fara tun ranar Laraba lokacin da dakarunsa suka cafke Bazoum tare da tsare shi a cikin fadar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye Na Sabbin Masu Rike Da Mukamai Masu Muhimmanci Da Gwamna Zulum Ya Rantsar

Tchiani tsohon na kusa da tsohon shugaban ƙasa Mahamadou Issoufou ne magabacin Shugaba Bazoum, wanda ya naɗa shi shugaban dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa a shekarar 2011.

Kamar yadda Channels TV ta rahoto, Bazoum ya bar shi akan muƙaminsa bayan ya karɓi mulki a hannun Issoufou, amma dangantaka ta yi tsami a tsakaninsu a cikin ƴan watannin da suka wuce, a cewar majiyoyi na kusa da Bazoum.

4. Janar Tchiani ya halarci yaƙe-yaƙe

Ya yi aiki a shirin samar da zaman lafiya na majalisar ɗinkin duniya da ƙungiyar ECOWAS a ƙasashen Ivory Coast da Sudan.

5. Kifar da yunƙurin juyin mulki a shekarar 2021 da 2022

Wani jami'in gwamnati ya bayyana cewa a bisa umarnin tsohon shugaban ƙasa Issoufou, Janar Tchiani ya mayar da dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa babbar runduna mai tarin manyan makamai.

Tchiani ya kifar da yunƙurin hamɓarar da gwamnatin farar hula, musamman a shekarar 2011 da 2022.

Kara karanta wannan

Ko Ganduje Zai Zama Shugaba? Jam'iyyar APC Ta Sanaya Ranakun Manyan Tarukanta 2

“General Tiani soja ne wanda ya nuna kansa a fagen daga." Cewar tsohon soja Amadou Bounty Diallo.

Janar Tchiani Ya Ayyana Kansa a Matsayin Shugaban Kasa

Rahoto ya zo cewa shugaban dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa a Jamhuriyar Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya ayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa.

Janar Tchiani ya ayyana kansa ne bayan sojoji a ƙarƙashin jagorancinsa sun kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng