Yanzu Yanzu: Tashin Hankali Yayin da Dakarun Tsaro Suka Garkame Shugaban Kasar Nijar Bazoum
- Rahotanni sun kawo cewa dakarun tsaro sun garkame shugaban kasa Mohamed Bazoum na jumhuriyar Nijar a fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai
- An tattaro cewa dakarun tsaron sun bi umarnin da rundunar sojoji ta bayar na kada su saki Shugaba Bezoum bayan tattaunawarsu ta wargaje
- Sai dai kuma, fadar shugaban kasar Nijar ta fitar da sanarwa cewa Bazoum da iyalinsa suna cikin koshin lafiya bayan afkuwar lamarin mara dadi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Yamai, Jumhuriyar Nijar- Rahotanni sun kawo cewa dakarun tsaro sun garkame Shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum, a cikin fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai, bayan umurnin da rundunar soji ta bayar.
Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, majiyoyi sun ce dakarun tsaron fadar shugaban kasar sun toshe duk wata hanyar zuwa gidan shugaban kasar da ofishoshi.
Majiyoyin sun ce dogarawan sun ki sakin shugaban kasar bayan tattaunawarsu ta wargaje.
"Rundunar sojin ta bayar da wani wa'adi," inji majiyar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An zabi Bazoum ta hanyar dimokradiyya a shekarar 2021 a karon farko na mika mulki ga zababben shugaba a kasar.
Da take martani, fadar shugaban kasar Nijar ta ce wasu jami'an tsaron fadar shugaban kasar sun fara wani yunkuri na gangamin kin jinin jamhuriya amma "a banza", rahoton Aljazeera.
A wata sanarwa da ta saki a ranar Laraba, 26 ga watan Yuli, fadar shugaban kasar ta bayyana cewa rundunar soji da dakarun kasar sun shirya farmakar wadanda ke da hannu a lamarin idan har yunkurin bai tafi daidai ba.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa shugaban kasa Bazoum da iyalinsa na cikin koshin lafiya.
Majiyoyin tsaron sun ce motocin sojoji sun toshe fadar shugagban kasar da ma'aikatu a safiyar Laraba, 26 ga watan Yuli.
An kuma tattaro cewa akwai kwanciyar hankali a birnin Yamai, babban birnin kasar.
Shugaban kasa Tinubu ya yi Allah wadai da yunkurin juyin mulki a Nijar
A halin da ake ciki, shugaba kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ba za ta amince da juyin mulki a Jamhuriyar Nijar ba.
Tinubu, wanda shi ne shugaban ƙungiyar ECOWAS ya bayyana haka ne a wata sanarwa da hadiminsa, D. Olusegun ya wallafa a shafinsa na Tuwita.
Asali: Legit.ng