Naira Ba Ta Cikin Kuɗaɗen Ƙasashe 10 Mafi Rauni a Afrika, Yayin Da CBN Ke Koƙarin Daga Darajarta
- Duk da faduwar darajar Naira a Najeriya, ba ta cikin jerin kudaden kasashe 10 da suka fi rauni a Afrika
- Leone na kasar Saliyo shi ne mafi raunin kudi a Afrika kuma na hudu mafi rauni a duniya
- Hawa da saukar kudade na shafar masu zuba jari na kasashen waje, 'yan yawon bude ido da ma gwamnatocin kasashe da dama
Kudin Najeriya wato naira, ba sa cikin jerin kudaden kasashe 10 na Afrika mafiya lalacewa a halin da ake ciki.
Hakan na da nasaba da matakai da dama da babban bankin Najeriya (CBN), ya dauka don ganin cewa ya kiyaye darajar naira.
Najeriya da wasu kasashen Afrika da dama na shan fama wajen daidaita farashin canjin kudadensu da na kasashen waje.
Sai dai duk da haka, Najeriya ba ta fado cikin jerin kasashen Afrika 10 da kudadensu suka fi na ko'ina lalacewa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kasashen Afrika 10 da kudadensu suka fi lalacewa a nahiyar
Legit.ng ta tattaro muku jerin kasashe 10 da kudadensu suka fi rauni a nahiyar Afrika idan aka musanyasu da dalar Amurka.
1. Sierra Leone (Dalar Amurka 1 = 17665.0 SLL)
Kamar yadda shafin Forbes ya nuna, kudaden kasar Saliyo su ne mafi lalacewa a nahiyar Afrika, kuma na hudu mafi rauni a duniya.
Kasar wacce ta yi iyaka da kasashen Laberiya da Gini, ta shahara wajen fitar da katakai, zinarai, daimon da sauran albarkatu na kasa.
Sai dai duk da wadannan abubuwan, ana gani tarin bashi, hauhawar farashin kayayyaki da kuma matsalar cutar Ebola da kasar ta fuskanta, na daga cikin abubuwan da ake ganin sun haddasawa kudin kasar lalacewa.
2. Guinea (Dalar Amurka 1 = 8509.00 GNF)
Kudin kasa Gini wato franc, su ne na biyu mafi rauni a nahiyar Afrika, sannan na takwas mafi lalacewa a duniya.
Allah ya albarkaci kasar ta Gini da albarkatun kasa masu tarin yawa, irinsu zinare da makamantansa.
Sai dai tsadar farashin kayayyaki da kuma rikice-rikicen jami'an soji da kuma shigowar 'yan gudun hijira daga kasar Laberiya da Saliyo, sun shafi tattalin arziki da kuma darajar kudaden kasar.
3. Madagascar (Dalar Amurka 1 = 4430.00 MGA)
Kudin kasar Madagaska wato MDA, su ne na uku mafi rauni a nahiyar Afrika. A baya kasar na amfani da Franc, kafin samar da MDA a shekarar 2005.
Madagaska na samun kudaden shiga daga bangaren noma, gandun daji da kuma harkokin kiwon kifi.
4. Uganda (Dalar Amurka 1 = 3665.00 UGX)
Kudaden kasar Uganda, wadanda aka fara amfani da su tun shekarar 1966, su ne na hudu mafi rauni a Afrika.
Uganda wacce ke a gabashin Afrika, ta hada iyakoki da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, Sudan ta Kudu, Kenya da Tanzania.
Allah ya albarkaci kasar da arzikin danyen mai, zinare da coffee, sai dai tulin bashi da rigingimu na siyasa sun hana kasar ci gaba.
5. Burundi (Dalar Amurka 1= 2806.96 BIF)
Kudaden franc na kasar Burundi, wadanda aka fara amfani da su tun shekarar 1964, sune na biyar mafi rauni a nahiyar Afrika.
Kasar Burundi ta yi iyaka da Tafkin Tanganyika, Rwanda, Tanzania da kuma Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.
Wani rahoto da bankin duniya ya fitar, ya nuna cewa kaso 80% na mutanen Burundi na gudanar da sana'ar noma ne.
6. Congo (Dalar Amurka 1 = 2476.00 CDF)
Kudaden kasar Kwango wato CDF, su ne na shida mafi rauni a Afrika. An fara amfani da su ne a kasar tun shekarar 1997.
Kasar tana samun mafi akasarin kudaden shigarta ne daga harkokin hakar ma'adinai da albarkatun kasa.
Kasar ta kan samu karin kudaden shiga ta bangaren noma, kiwo da kuma harkokin gandun daji.
7. Tanzania (Dalar Amurka 1 = 2440.00 TZS)
Kudaden kasar Tanzaniya wato TZS, sune na bakwai mafiya rauni a cikin jerin kudaden kasashen 10 na Afrika.
“Kana Da Karfin Hali”: Malamar Jami’ar Najeriya Ta Fashe Da Kukan Murna Yayin da Dalibinta Ya Nemi Aurenta a Bidiyo
Kasar tana samun kudaden shigarta daga bangaren masu zuwa yawon bude idanu, hakar ma'adinai, da kuma bangaren noma.
8. Rwanda (Dalar Amurka 1 = 1159.60 RWF)
Franc na kasar Rwanda sune kudade na takwas mafi rauni a nahiyar Afrika.
Akalla kaso 70% na al'ummar kasar ta Rwanda duk manoma ne, kamar yadda wani rahoto na The Borgen Project ya nuna.
9. Malawi (Dalar Amurka 1 = 1043.020 MWK)
Kwacha shi ne sunan kudin kasar Malawi, wanda aka fara amfani da shi tun shekarar 1970.
Kudaden na Malawi sune na tara a cikin jerin kudaden kasashe 10 mafi rauni a nahiyar Afrika.
Kasar ta fi mayar da hankali kan bangaren noma wajen samun kudaden shiga.
10. South Sudan (Dalar Amurka 1 = 979.067 SSP)
Kudaden Sudan ta Kudu wato SSP, sune na 10 mafi lalacewa a cikin jerin kudaden kasashe 10 na Afrika mafi rauni.
Wani rahoto na bankin raya kasashen Afrika, ya nuna cewa kaso 80% na mutanen Sudan ta Kudu duk manoma ne.
Sabbin attajiran da ke marawa Aiko Dangote baya a nahiyar Afrika sun bayyana
Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto kan karin attajiran da suka mallaki biliyoyin daloli baya ga Aliko Dangote, a nahiyar Afrika.
An bayyana cewa nahiyar ta Afrika na da masu kudi 46, da suka mallaki abinda ya haura dalar Amurka biliyan daya.
Asali: Legit.ng