Wata Hajiya Daga Jihar Legas Ta Sake Rasuwa a Kasa Mai Tsarki

Wata Hajiya Daga Jihar Legas Ta Sake Rasuwa a Kasa Mai Tsarki

  • Allah ya yi wa wata Hajiya mai shekara 70 a duniya rasuwa a ƙasa mai tsarki bayan kammala aikin Hajjin bana
  • Hajiyar wacce ta fito daga jihar Legas ta rasu ne a yayin da ta ke ƙoƙarin tsallaka wani babban titi a ƙasa mai tsarki
  • Rasuwar Hajiyar ya sanya adadin Alhazan Najeriya da suka rasu a ƙasa mai tsarki a Hajjin bana ya kai mutum 15

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Saudiyya - Wata Hajiya da ba a bayyana sunanta ba mai shekara 70 a duniya ta rasu a ƙasa mai tsarki bayan kammala aikin Hajjin bana na shekarar 2023.

Hajiyar wacce ta fito daga jihar Legas ta koma ga mahaliccinta ne bayan ta yanke jiki ta faɗi, jaridar Nigerian Tribune ta yi rahoto.

Wata Hajiya 'yar Najeriya ta sake rasuwa a Saudiyya
Hajiyar mai shekara 70 ta fito ne daga jihar Legas Hoto: @HaramainInfo
Asali: Twitter

A cewar sahihan bayanai, marigayiyar ta yanke jiki ta faɗi ne lokacin da ta ke ƙoƙarin tsallaka wani babban titi a kusa da otal ɗin da aka sauke Alhazan da suka fito daga jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Hare-Haren 'Yan Bindiga: Dan Majalisar Tarayya Ya Buƙaci Mutanen Jiharsa Su Kare Kansu

Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 5:00 na Asuba (agogon Najeriya) wanda hakan ya jefa Alhazan shiga cikin halin jimamin rasuwarta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ƙoƙarin farfaɗo da Hajiyar da aka yi bai yi nasara ba yayin da ta rasu akan hanyar kai ta zuwa asibiti.

Alhazan Najeriya 14 sun rasu a Saudiyya

Tawagar likitocin hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), ta bayyana cewa Alhazan Najeriya 14 ne suka riga mu gidan gaskiya a yayin aikin Hajjin Bana, cewar rahoton PM News.

A cewar tawagar bakwai daga cikin Alhazan sun rasu ne kafin ranar Arafat, shida sun rasu a lokacin Mashair, yayin da mutum ɗaya ya sake rasuwa bayan ranar Arafat.

Rasuwar wannan Hajiyar ta sanya adadin yawan Alhazan Najeriya da ya suka rasu a ƙasa mai tsarki ya kai mutum 15.

Alhazan Kano Sun Barke Da Gudawa a Makkah

Kara karanta wannan

An Shiga Rudani Yayin da Jami'an Amotekun Suka Halaka Wani Mahauci Dan Jihar Sokoto a Oyo

A wani labarin na daban kuma, Alhazan da suka fito daga jihar Kano sun ɓarke da gudawa a ƙasa mai tsarki bayan kammala aikin Hajjin bana.

Hukumomi sun sanar da cewa Alhazai tara ne suka ɓarke da guduwa bayan sun ci abincin Takaru a ƙasa mai tsarki, inda aka basu magunguna domin shawo kan matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel