Wata Hajiyar Najeriya Ta Rasu a Saudiyya Bayan Kammala Aikin Hajjin Bana
- Allah ya yi wa wata dattijuwar Hajiya daga jihar Legas rasuwa bayan an kammala aikin Hajjin bana a ƙasa mai tsarki
- Hajiyar mai shekara 66 a duniya ta koma ga mahaliccinta ne kwana ɗaya bayan an fara jigilar dawo da Alhazan Najeriya zuwa gida
- Tuni aka yi mata jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada, yayin da ake jiran sakamakon bincike kan musabbabin rasuwarta
Saudiyya - Wata Hajiya mai shekara 66 a duniya daga cikin Alhazan Najeriya ta riga mu gidan gaskiya, dattijuwar ta rasu ne washegarin ranar da Alhazan Najeriya suka fara dawowa gida bayan kammala aikin Hajjin shekarar 2023.
Jaridar Aminiya ta kawo rahoto cewa wata Hajiya wacce su ke zaune a ɗaki ɗaya da marigayiyar ne ta tsinci gawar dattijuwar a banɗaki bayan ta zagaya yin tsarki.
Mahajjaciyar Najeriya Ta Tsinci Miliyan 56 a Saudiyya, Ta Mikawa Hukumar Jin Dadin Alhazai Na Zamfara
A wannan aikin Hajjin na bana, akwai Alhazan Najeriya kimanin mutum 15 da suka riga mu gidan gaskiya tun bayan da aka fara aikin Hajjin daga cikin Alhazai sama da 1.8m da suka sauke farali a bana.
An yi jana'izarta kamar yadda addinin musulunci ya tanada
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An yi jana'izar marigayiyar mai suna Alhaja Kuburat Sekoni wacce ta fito daga ƙaramar hukumar Oshodi a jihar Legas.
Amirul Hajj na Jihar Legas, Anofiu Elegusi, da yake tabbatar da rasuwar Hajiyar, ya yi bayanin cewa sai da suka miƙa gawar marigayiyar ga hukumar NAHCON, kafin daga bisani aka kai ta makwancinta.
Dangane da musabbabin rasuwar marigayiyar, Amirul Hajjin ya ce suna kan tuntuɓar hukumar NAHCON “saboda alhakin tattaunawa da ma’aikatar lafiya ta ƙasa mai tsarki a wuyanta ya rataya domin bincike da kuma sanar da dalilin rasuwar,” wacce ta auku a ranar Laraba.
Innalillahi: Amarya Yar Shekara 21, Maimunatu Ta Caka Wa Angonta Wuka Har Lahira Kan Karamin Abu a Bauchi
Ya yi bayanin cewa hukumomi suna kammala bincikensu za a bayyana sakamakon abin da binciken ya gano.
Aniofu ya aike da saƙon ta'aziyyar gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, wanda ya nuna kaɗuwarsa kan rasuwar marigayiyar inda ya yi addu'ar Allah ya rahamshe ta, cewar rahoton Tribune Online.
Hajiya Ta Mayar Da N56m Da Ta Tsinta a Saudiyya
A wani labarin na daban kuma wata Hajiya da ta fito daga jihar Zamfara, ta tsinci maƙudan kuɗaɗe har dala 80,000 (N56m) a ƙasa mai tsarki.
Hajiya Aishatu Ƴan Guru Nahuce wacce ta fito daga ƙaramar hukumar Bungud ta mayr da kuɗin ba tare da taɓa ko sisi ba.
Asali: Legit.ng