Babu 'Yan Najeriya a Ciki, Attajiran Nahiyar Afirika 4 Suka Yi Alkawarin Sadaukar Da Kaso 50% Na Dukiyarsu

Babu 'Yan Najeriya a Ciki, Attajiran Nahiyar Afirika 4 Suka Yi Alkawarin Sadaukar Da Kaso 50% Na Dukiyarsu

  • Attajirai da dama na sadaukar da kaso mai tsoka na dukiyarsu domin magance wasu matsaloli a duniyar nan
  • Aƙalla akwai attajirai 200 da suka yi wannan sadaukarwar waɗanda suka haɗa da irinsu Bill Gates, Mark Zuckerberg, Elon Musk, and Warren Buffett
  • Wasu attajiran nahiyar Afirika waɗanda jimillar dukiyarsu ta kai N5trn su ma sun bi sahu wajen sadaukar da dukiyarsu

Wasu attajiran nahiyar Afirika huɗu na daga cikin mutanen da a faɗin duniya suka ɗauki alƙawarin sadaukar da kaso mai tsoka na dukiyarsu domin yin ayyukan sadaka.

Wannan tsarin dai Bill Gates da Warren Buffet suka fara shi a shekarar 2010 da niyyar sanya attajiran duniya su bayar da aƙalla rabin dukiyoyinsu suna a raye ko a cikin wasiyyarsu.

Attajiran Afirika huɗu da za su sadaukar da dukiyarsu
LR- Mo Ibrahim, Mohammed Dewji, Patrice Motsepe, Strive Masiyiwa Hoto: Forbes
Asali: Facebook

Yana da kyau a sani cewa wannan sadaukarwar ba dole bace kawai ganin kyautuwar hakan ne ya sanya su ke yi.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 6 Da Ya Kamata Ku Sa Game Da Sabon Sufeto Janar Na 'Yan Sanda, Egbetokun Olukayode

Attajiran nahiyar Afirika da suka shiga cikin wannan sadaukarwar sun haɗa Patrice Motsepe, Mohammed Ibrahim, Mohammed Dewji, daStrive Masiyiwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Binciken Legit.ng ya nuna a cewa ya zuwa ranar Talata, 20 ga watan Yunin 2023, attajiran huɗu suna da jimillar dukiya wacce ta kai $7.2bn (dai dai da fiye da N5trn idan aka yi amfani da $1/N750)

Patrice Motsepe

Patrice Motsepe attajiri ne ɗan ƙasar South Africa wanda yake harkokin haƙar ma'adanai da wasanni.

Shi ne ɗan Afirika na farko da ya fara fitowa a cikin jerin attajiran duniya na Forbes amma yanzu shi ne na 1213 ya zuwa ranar Talata, 20 ga watan Yunin 2023 inda yake da dukiyar da ta kai $2.6bn.

Mohammed Ibrahim

Mohammed Ibrahim shi ma wani ɗan Afirika ne wanda yake a cikin jerin daga ƙasar Sudan sannan yana da fasfo na ƙasar Burtaniya.

Kara karanta wannan

Dan Sandan Da Ya Dawo Da $800 Na Wata Hajiya a Katsina, Ya Samu Kyautar Da Ba Zai Taba Mantawa Da Ita Ba a Rayuwarsa

Ya tara dukiyarsa ta hanyar sadarwa. Forbes ta sanya shi a matsayi na 2414 a cikin jerin attajiran inda yake da dukiyar da ta wuce $1.2bn.

Mohammad Devji

Mohammed Devji ɗan ƙasar Tanzania ne wanda ya samu dukiyarsa ta hanyar sadarwa.

Devji ganzu haka yana da dukiya wacce a ranar Talata, 20 ga watan Yuni ta kai $1.5bn.

Strive Masiyiwa

Strive Masiyiwa wani attajiri ne ɗan ƙasar Zimbabwe mazaunin birnin Landan wanda ya samu dukiyarsa ta hanyar sadarwa da noma.

Forbes ta sanya shi a matsayin attajiri na 1,673 a cikin jerin attajiran duniya inda yake da dukiya wacce ta kai $1.8bn.

An Ƙabar Da Dangote Daga Matsayin Wanda Yafi Kowa Kudi a Afirika

A wani labarin, hamshaƙin attajirin nan Aliko Dangote ya rasa matsayinsa na wanda ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika bayan ya daɗe akan matsayin.

Kara karanta wannan

Dubun Masu Satar Awaki Ta Cika A Gombe Yayin Da 'Yan Sanda Suka Yi Ram Da Su

Rahoton Forbes ya nuna cewa ɗan ƙasar South Africa, Johann Rupert, shi ne attajirin da ya doke Dangote daga matsayin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng