Elon Musk Ya Sake Komawa Attajirin Da Ya Fi Kowa Kudi a Duniya, Dangote Ya Koma Matsayin Na 72

Elon Musk Ya Sake Komawa Attajirin Da Ya Fi Kowa Kudi a Duniya, Dangote Ya Koma Matsayin Na 72

  • Elon Musk ya sake komawa kan matsayinsa na attajirin da ya fi kowa kuɗi a duniya daga hannun Bernard Arnault
  • Musk ya samu kusan $1bn inda ya doke Arnault daga matsayin na farko bayan Arnault ya yi asarar $5bn a ranar Laraba, 31 ga watan Mayun 2023
  • Wanda ya fi kowa arziƙi a Najeriya, Aliko Dangote, ya koma matsayi na 72 a ranar Laraba bayan ya samu N24.4bn cikin kwana ɗaya

Shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk, ya koma matsayin attajirin da yafi kowa kuɗi a duniya, inda ya karɓe kambun daga hannun ɗan kasuwar ƙasar Faransa Bernald Arnault.

Musk, wanda ya samu sama da $1bn cikin sa'o'i 24, ya karɓe kambun daga hannun ɗan ƙasar Faransan wanda ya riƙe kambun har na tsawon fiye da wata shida.

Kara karanta wannan

Arzikin Dangote Ya Yi Tashin Gwauron Zabi, Ya Koma Cikin Jerin Hamshakan Attajirai 70 a Duniya

Elon Musk ya koma attajirin da ya fi kowa kudi a duniya
Elon Musk da Aliko Dangote Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

Kamfanin motocin Elon Musk ya samu tagomashi

Sabon shugaban na Twitter, ya samu wannan tagomashin ne bayan an siyar da hannun jarin kamfanin motocinsa na Tesla akan $203.93 a ranar Laraba, 31 ga watan Mayu 2023, wanda hakan ya sanya arziƙinsa ya kai $192 billion.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A na sa ɓangaren, Arnault ya koma matsayin na biyu ne bayan ya yi asarar $5bn cikin sa'o'i 24, inda arziƙinsa ya koma $187 bn.

Musk wanda yanzu haka yana ƙasar China domin tattaunawa da hukumomi kan matsayar motocinsa masu amfani da lantarki, ya tserewa Arnault da $5bn.

Dangote ya koma matsayi na 72 a jerin attajiran duniya

Haka kuma, attajitin da ya fi kowa kuɗi a Najeriya da nahiyar Afirika, Aliko Dangote, ya ƙara matsawa sama a cikin jerin attajirin duniya da mataki uku, a ranar Laraba, 31 ga watan Mayun 2023.

Kara karanta wannan

"Tallafin Man Fetur Ya Tafi," Shugaba Tinubu Ya Fara Ɗaukar Matakai Masu Tsauri

Hamshaƙin attajirin na Najeriya, yanzu yana a matsayi na 72 a cikin jerin hamshaƙan attajiran duniya, a cewar ƙididdigar Bloomberg.

Shugaban rukunonin kamfanin Dangote, ya samu $53.2m kusan N24.4bn a ranar Laraba inda ya koma matsayi na 75 da ya taɓa riƙewa a baya.

Legit.ng ta tattaro cewa Dangote ya koma na 75 ne bayan ya baro matsayi na 84 a cikin jerin attajiran na duniya a ranar Talata, 30 ga watan Mayun 2023.

Arzikin Dangote Ya Yi Tashin Gwauron Zabi

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa arziƙin hamshaƙin attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika, Aliko Dangote, ya ƙaru sosai a cikin kwana ɗaya kacal.

Dangote ya samu $769m a cikin kwana ɗaya wanda hakan ya sanya ƙara matsawa sama a cikin jerin hamshaƙan attajiran da suka fi kowa kuɗi a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng