Fasinja Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ya Buɗe Jirgin Sama Ana Tsaka Da Tafiya a Sararin Samaniya

Fasinja Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ya Buɗe Jirgin Sama Ana Tsaka Da Tafiya a Sararin Samaniya

  • Wani mutum ɗan kimanin shekaru 30 ya buɗe ƙofar fita ta gaggawa a cikin jirgin saman kamfanin Asiana ana tsaka da tafiya a saman saboda a cewarsa, ya ji numfashinsa na neman ɗaukewa
  • ‘Yan sandan Daegu ne suka kama mutumin domin yi masa tambayoyi kuma ana ganin zai iya fuskantar ɗaurin shekaru 10 a gidan yari saboda ya saɓawa dokokin kiyaye lafiyar jiragen sama
  • An kwantar da fasinjoji 12 a asibiti bayan fuskantar matsalar numfashi da suka yi, amma ba su samu wasu manyan raunuka

Koriya ta Kudu - Wani mutum da ya bude kofar fita ta gaggawa a jirgin saman Asiana ana tsaka da sheƙa gudu a sama ya bayyana cewa numfashinsa ne ya ji yana neman ɗaukewa, sai ya bude domin ya sha iska.

Jirgin mai ɗauke da fasinjoji kusan 200 ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Daegu mai tazarar kilomita 240 kudu maso gabashin birnin Seoul babban birnin Koriya ta Kudu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Daga Ƙarshe, Jirgin Saman Najeriya Ya Sauka a Birnin Abuja, Bidiyo

Fasinjan jirgin sama da ya bude kofa ya ce iska zai sha
Fasinja ya ce shan iska ya ke son yi shi yasa ya bude jirgin sama a sararin samaniya. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Saura sa'a ɗaya jirgin ya sauka a lokacin da abin ya faru

A rahoton da BBC ta wallafa, lamarin ya faru ne a ranar Juma'a inda jirgin ya taso da fasinjoji 194 daga wani filin da ke Jeju Island.

Mutumin ɗan kimanin shekaru 30 ya buɗe ƙofar a lokacin da jirgin ke sama da mita 200 (kafa 650) a sama. Mahukunta sunce bai wuce saura sa'a ɗaya jirgin ya sauka ba a lokacin da abin ya faru.

Sai dai jirgin ya sauka lafiya ba tare da asarar ran ko mutum ɗaya ba, sai dai wasu sun samu ƙananun raunuka da kuma fargaba.

Korarsa aka yi daga wajen aiki

'Yan sandan Daegu sun kama fasinjan bayan saukar jirgin domin yi masa tambayoyi, a inda ya shaida musu cewa yana cikin damuwa ne sakamakon rasa aikinsa da ya yi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Ɗebo da Zafi, Ya Fallasa Masu Satar Dukiyar Talakawa a Kusa da Buhari

Ya kuma shaida musu cewa ya ga jirgin ya ɗauki tsawon lokaci fiye da yadda ya kamata, wanda hakan yasa ya ji numfashinsa na neman ɗaukewa, kamar yadda Punch ta wallafa.

Masana doka sun ce fasinjan na iya fuskantar ɗaurin shekaru 10 a gidan yari saboda saɓa dokokin kiyaye lafiyar jiragen sama.

Wani faifan bidiyo da wani fasinja da ke kusa da wurin ya ɗauka, ya nuna yadda iska ta riƙa shigowa cikin jirgin tare da hura rigunan kujerun jirgin da kuma yamutsa gashin fasinjojin.

An kwantar da fasinjoji 12 a asibiti

An kwantar da fasinjoji 12 a asibiti sakamakon matsalar numfashi da suka fuskanta, amma ba su samu wasu manyan raunuka ba, a cewar ma'aikatar sufuri.

Wani jami'in ma'aikatar sufuri ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa wannan shi ne karo na farko da suka taɓa ganin irin haka a tarihin jiragen sama na Koriya.

Masana sun ce masana'antar sufurin jiragen sama ta Koriya ta Kudu na da ingantaccen tarihi a ɓangaren tsaro.

Kara karanta wannan

“Na Fi Karfin Mace Daya”: Wani Mutum Dan Shekara 63 Mai Mata 15 Da Yara 107 Ya Ce Zai Kara Aure

Jirgin sama ya yi saukar gaggawa a Abuja

Ko a kwanakin baya sai dai Legit.ng ta kawo muku rahoton wani jirgi na Max Air da ya yi saukar gaggawa a filin tashi da saukar jirage na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Jirgin wanda ya taso daga garin Yola babban birnin jihar Adamawa ya yi saukar gaggawar ne sakamakon kamawa da wuta da tayoyinsa suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng