Abin Farin Ciki: An Gano Yaron Da Ya Ɓata Watanni 2 Baya Daga Kano A Ƙasar Togo
- An samu nasarar gano wani yaro mai shekaru 14 da ya ɓata daga gidansu da ke Hotoro, jihar Kano, watanni biyu baya a ƙasar Togo
- An samu yaron tare da wani yaron da shi ma ya bayyana cewa daga Najeriya yake suna ta gararamba a kan titin ƙasar ta Togo
- Mahaifin yaron ya nemi taimakon al'umma sabili da ba ya da halin iya dawo da yaron gida daga can inda aka gano shi
Kano - An samu nasarar gano wani yaro ɗan kimanin shekaru 14, wanda ya ɓata daga birnin Kano watanni biyu da suka gabata a ƙasar Togo.
Iyayen yaron da ke a unguwar Hotoro sun sanar da ɓatan yaron nasu a wani lokaci cikin watan Mayun da ya gabata.
An gano yaran ta dalilin wata mai siyar da abinci
Kamar yadda gidan rediyon Freedom da ke Kano ya bayyana, an gano yaron ne su biyu da wani yaron da shi ma asalin ɗan Najeriya ne suna ta gararamba kan titi domin neman abinda za su ci a ƙasar ta Togo.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An gano yaran ne ta dalilin wata sananniyar mai siyar da abinci a Togo mai suna Hajiya Maijidda Mai Abinci, wacce ta ce wasu mutane ne suka kawo mata yaran sakamakon bayyana musu da suka yi cewa su 'yan Najeriya ne.
Wata mata ce ta taho da su daga Najeriya zuwa Ghana
Hajiya Maijidda ta ƙara da cewa yaran sun shaida ma ta cewa wata mata ce ta taho da su daga Najeriya ta kai su zuwa ƙasar Ghana domin su riƙa taya ta bara.
Yaran sun bayyana cewa daga bisani matar da ta taho da su ɗin ta rabu da su suna ta garari wanda a cikin hakan ne har suka tsinci kansu a ƙasar ta Togo, kamar dai yadda Daily Trust ta haƙaito.
Maijidda ta bayyana cewa ta ajiye yaran a hannunta tana kula dasu, sannan kuma sai ta tuntuɓi wasu 'yan Najeriya da ke gida domin ganin an nemo ma ta iyayen yaran.
Mahaifin yaron ya bayyana farin cikinsa da nuna godiya ga Hajiya Maijidda, sannan kuma ya nemi al'umma da su taimaka masa da kuɗin motar da zai aika a dawo da yaron nasa gida.
Ya ƙara da cewa sun shiga matukar damuwa gami da shan ɓaƙar wahala a waɗannan watanni biyu da suka yi suna neman yaron nasu, daga nan ya yi godiya ga Ubangiji bisa bayyana masa yaronsa da ya yi.
Mata sunyi zanga-zanga kan ɓatan yara a Kano
A cikin shekarar 2021 ne dai mata a cikin birnin Kano suka fito kan titi ɗauke da takardu suka gudanar da zanga-zanga dangane da yawaitar bacewar yara da ake samu a jihar ta Kano.
Matan sun dai gudanar da zanga-zangar ne domin nuna ɓacin ransu bisa abinda suka kira sakacin hukuma wajen kasa dawo musu da yaran su da suka ɓata.
Asali: Legit.ng