Mata a Kano sun yi zanga kan batan yara (Hoto)

Mata a Kano sun yi zanga kan batan yara (Hoto)

- Mata da dama a Jihar Kano sun fito sunyi zanga-zangar nuna damuwa kan yaransu da suka bata

- Matan sun koka cewa yaransu kimanin 118 ne aka sace aka sayar a wasu sassan Najeriya tun shekarar 2016

- Matan sun fito rike da takardu da kuma hotunan yaran sunyi tattaki zuwa hukumar karbar korafi da giajen watsa labarai

Matan da yaran su suka bata a Kano sunyi zanga zanga a Kano ranar Laraba akan abin da suka kira sakacin hukumomi wajen mayar da hankali don dawo musu da yaran su, Daily Trust ta ruwaito.

Matan rike takardu da banoni da kuma hotunan yaran da suka bata, sun kai ziyara hukumar karbar korafi da yaki da cin hanci da rashawa, ma'aikatar al'amuran mata da kuma gidajen jaridu don mika koken su.

Mata a Kano sun yi zanga kan batan yara
Mata a Kano sun yi zanga kan batan yara. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Zainab Abdullahi Giginyu, ta ce, "mun gaji da wannan al'amarin. shekaru da dama muna korafi, amma gwamnati ta nuna halin ko in kula."

DUBA WANNAN: Kungiyar kwallon kafa ta Nasarawa United ta bayyana bacewar dan wasan ta

A cewar ta, daga 2016 zuwa yanzu, matar ta bayyana bacewar yara 118 kuma an yarda cewa sace su akayi aka siyar a wani bangaren kasar nan.

Ta ce mafi yawancin yaran sun fito ne daga unguwannin Hotoro, Kawo, Yankaba da Gama da ke jihar, ta na cewa "abun ya dame mu kwarai kuma muna son gwamnati ta yi duk mai yiwuwa don ganin yaran mu sun dawo."

"Muna sane da kwamitin da gwamnatin ta kafa, amma bamu ji ko mun ga wani abu da suka dauka akan al'amarin ba", a cewar ta.

A jawaban da suka gabatar, kwamishinar mata ta jihar, Zaharau Mohammed da kuma shugaban hukumar karbar korafi, Barrister Muhuyi Rimin Gado, sun tabbatar wa matan cewa gwamnatin jihar zata yi duk mai yiwuwa don ganin yaran su sun dawo cikin koshin lafiya.

KU KARANTA: Abinda yasa na bari wani daban ya yi min ciki a gidan mijina, matar aure

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa lamarin batan yara ya dade yana addabar jihar, an taba kama wasu da ke da alaka da satar yaran kuma an gurfanar da su.

A watan Yunin shekarar da mu ke bankwana da ita, gwamna Abdullahi Ganduje ya kaddamar da kwamiti don su tattara bayani akan wasu yara da aka sata aka kuma siyar da su a jihar Amambra a 2019.

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: