Sarki Charles III: Zafafan Hotuna 7 Yayin Da Aka Nada Sabon Sarkin Ingila Tare Da Matarsa
- Kamar yadda aka yi zato, naɗin sarautar sarki Charles III da sarauniya Camilla, ya ƙayatar sosai
- Tun daga faretin sojoji zuwa yin abubuwan da al'ada ta tanada, naɗin sarautar abin kallo ne
- Naɗin sarki Charles III kamar na mahaifiyarsa sarauniya Elizabeth II, zai taka muhimmiyar rawa sosai ta ɓangarori da dama
Birnin Landan - Daga ƙarshe dai an naɗa sarki Charles III matsayin sabon sarkin Burtaniya da daular ta, wanda hakan ya buɗe sabon shafi a masarautar.
Duk da yanayin ruwa da ake ciki a wajen taron, dandazon mutane sun fito da ƙwarin guiwar su domin halartar naɗin sarautar.
1. Dandazon mutane
Dandazon mutane sun taru a wajen fadar Buckingham domin ganin naɗin sarautar.
Ɗauke da laimomin su da rigunan kare ruwa, dandazon mutanen sun riƙa ɗaga tutocin UK, yayin da su ke jiran a fara naɗin sarautar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
2. Faretin sojoji
Faretin sojoji ya ƙayatar da taron sosai wanda aka gudanar mai cike da ɗumbin tarihi.
Aƙalla sojoji 4000 daga ƙasashe rainon Ingila suka riƙa wucewa ta kan tituna kamar yadda ya ke a al'ada.
3. Gimbiya Ann ta hau doki
Mai tsaron lafiyar sarkin, gimbiya Anne, ta biyo tawagar sabon sarkin akan doki.
Itace kaɗai yar gidan sarautar da ta hau kan doki, yayin da sauran su ke akan abin hawa.
4. Sarki Charles da sarauniya Camilla sun ɗago hannu
Kamar yadda ya ke a al'ada, sarki Charles III da sarauniya Camilla sun hau kan baranda domin ɗagowa dandazon mutane hannu
5. An tuƙa sarki Charles III da sarauniya Camilla a cikin motar zinare
Sarki Charles III da sarauniya Camilla an tuƙa su a cikin motar zinare wacce aka ƙera a 1760, sannan ake amfani da ita a kowane naɗin sarauta tun daga kan na William IV a shekarar 1831.
An fara tuƙa ta ne daga Westminster Abbey zuwa fadar Buckingham, yayin da suke ta ɗagowa dandanzon mutanen da suka taru akan hanya hannu.
6. Yarima Harry ya halarci naɗin sarautar
Yarima Harry, ɗan sarkin Charles III na biyu, ya halarci naɗin sarautar mahaifinsa duk da cewa ya nuna baya son sarautar da aka ba shi.
Yariman ya iso Westminster Abbey ne tare da ƴan'uwan sa.
7. Jill Biden ta wakilci shugaba Biden
Shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden ya riƙe al'ada inda ya ƙi halartar naɗin sarautar sabon sarkin, duk kuwa da dangantaka mai kyau da ke a tsakanin ƙasashen biyun.
Sai dai, matarsa Jill Biden, ta wakilce shi a wajen naɗin sarautar.
Bola Tinubu Ya Aika Wasika Ta Musamman Ga Sabon Sarkin Ingila
A wani rahoton na daban kuma, zaɓaɓɓen shugaban ƙasan Najeriya, Bola Tinubu, ya aike da wasiƙa ga sabon sarkin Ingila.
Bola Tinibu ya taya sabon sarkin murnar naɗin sarautar da aka yi masa, sannan ya yi fatan kyakkyawar dangantakar da ke a tsakanin Najeriya da Ingila, ta cigaba da wanzuwa.
Asali: Legit.ng