Yan Bindiga Sun Yi Wa Messi Barazana, Sun Kai Wa Yan Uwan Matarsa Hari
- Wasu yan bindiga biyu sun bi dare tare da kai hari kan wata kasuwar zamani mallakar iyalan matar Lionel Messi
- Yan bindigan sun bar sakon barazana ga fittaccen dan wasan kwallon kafar tare da bayyana cewa shugaban garin su Javkin ba zai ya ceton sa ba
- Javkin ya bayyana cewa an kai harin ne don hada hayaniya a garin kasancewar babu labarin da zai fi saurin yaduwa fiye da kai wa Messi hari
Rosario, Argentina - Cikin dare, wasu yan bindiga su biyu sun bude wuta a wata kantin zamani mallakar iyalan matar Messi, kafin barin sakon barazana a wajen kan fittaccen dan wasan kwallon kafa da ya lashe kyautar Ballon d'or bakwai, Daily Trust ta rahoto.
Maharan sun yi wani rubutu a kasa da hannu bayan sun harba harsashi 14 kan kofar babban kantin zamanin da safiyar ranar Alhamis 2 ga watan Maris na 2023, rubutun ya ce:
''Messi, muna jiranka. Javkin dilallin miyagun kwayoyi ne, ba zai kula da kai ba."
Pablo Javkin shi ne shugaban garin su Messi, Rosario, inda kantin zamanin take, kilomita 320 Arewa maso yammacin Buenos Aires.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Javkin ya tabbatar da cewa kantin zamanin mallakar iyalan Antonela Roccuzzo ce, wadda ke da yaya uku tare da fittaccen dan wasan kwallon kafar, kuma ya ce an kai harin ne ''don a haddasa rikici a birnin.''
''Yanzu, wani irin shirme ne haka, abin takaici ne,'' a cewarsa. ''Wanne labari ne zai fi saurin yaduwa a duniya fiye da kai wa Messi hari?''
Wani da ya shaida lamarin ya tabbatar da ganin yan bindigar sun isa wajen akan babur daf da karfe 3:00 na dare. Daya daga ciki ya sauka, ya fara harbi, ya bar sakon rubutun sannan suka gudu, rahoton Al Jazeera.
Javkin ya ce:
''Ana yawan yin haka a wasu lokuta, muna da hukumomin tsaro guda biyar a Rosario amma za su iya haka saboda ba wanda zai bi sahun su."
Na yi da na sanin zana tattoo din Messi a goshi na, matsala ya janyo min, Jambs
Mike Jambs, wanda ke da karfin fada a ji a dandalin sada zumunta ya bayyana cewa ya yi nadamar rubuta sunan Lionel Messi a fuskarsa bayan Argentina ta lashe kofin duniya.
Jambs, wanda masoyin Messi ne ya rubuta sunansa a goshinsa da kumatunsa domin ya nuna farin cikinsa da kaunarsa kamar yadda Daily Mail ta rahoto.
Asali: Legit.ng