Ana Awa 48 Zabe, Shugaban Amurka Joe Biden Ya Aika Muhimmin Sako Ga Al'ummar Najeriya Da Yan Takara

Ana Awa 48 Zabe, Shugaban Amurka Joe Biden Ya Aika Muhimmin Sako Ga Al'ummar Najeriya Da Yan Takara

  • Shugaban Amurka, Joe Biden, ya jinjinawa yan takarar shugaban kasa da za su fafata a zaben 2023 saboda rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya
  • Shugaban na Amurka yana ganin yan Najeriya sun cancanci su zabi wanda zai jagorance su a gaba a zaben da ke tafe
  • A cewar Biden, gwamnatin Amurka ta ba goyon bayan kowanne dan takara amma tana goyon bayan zabe na zaman lafiya, adalci da nagarta

A yayin da aka yi nisa wurin shirye-shiryen babban zaben shekarar 2023, shugaban Amurka, Joe Biden, a ranar Alhamis, 23 ga watan Fabrairu, ya ce yan Najeriya sun cancanci zaben shugaba da zai jagorance su a gaba.

Biden a cikin sanarwar da ofishin jakadancin Amurka ta fitar a Najeriya da Legit.ng ta gani ya yaba wa yan takarar shugaban kasa saboda raka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Zaben bana: Sheikh Dahiru Bauchi ya fadi dan takarar da 'yan Tijjiniya za su zaba ranar Asabar

Joe Biden
Shugaban Amurka ya aika sako ga yan Najeriya ana kwana biyu zabe. Hoto: Photo credit: Anna Moneymaker
Asali: Getty Images

Shugaban na Amurka ya ce ta hanyar rattaba hannu kan yarjejeniyar, jam'iyyun da yan takarar sun nuna cewa za su amince da sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta INEC za ta yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya kuma ce abin da yan takarar shugaban kasar suka yi ya nuna cewa suna goyon bayan mika mulki zuwa sabuwar gwamnati cikin lumana bayan sakamakon zaben na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu, da za a yi a sassan kasar.

Yan Najeriya sun cancanci su zabi shugaban da zai jagorance su

Bayan cewa yan kasar suna da dukkan dama da iko na zaben wanda zai tafiyar da harkokinsu na kasa, Biden ya ce zabe wani ginshiki ne mai muhimmanci na dimokradiyya.

Wani sashi na kalamansa:

"Yayin da Amurka ba ta goyon bayan kowanne dan takara ko jam'iyya, muna goyon bayan zabe na zaman lafiya da adalci wanda zai nuna abin da yan Najeriya ke so.

Kara karanta wannan

Zaben jibi: Rudunar soja ta fitar da sako mai daukar hankali ga dukkan 'yan Najeriya

"A ranar zabe, ina shawartar dukkan yan Najeriya - ba tare da la'akari da addini ko yanki ko kabila ba - su fita su sauke nauyin da ke kansu - har da matasa, wasu daga cikinsu wannan shine karon farko da za su yi zabe."

Sufeta Janar na yan sandan Najeriya ya bada umurnin takaita zirga-zirga a ranar zabe

A gefe guda, Usman Alkali Baba, sufeta janar na yan sandan Najeriya ya bada umurin takaita zirga-zirgan ababen hawa a titi, ruwa da sauran nau'ika a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu saboda zabe.

Shugaban yan sandan ya ce wadanda kawai aka bari su yi zirga-zirgan suna masu muhimman ayyuka kamar masu sa ido kan zabe, motar daukan marasa lafiya, motar kashe gobara da sauransu.

Baba ya ce an dauki matakin ne saboda tabbatar da tsaron masu zabe, tafiyar da zaben cikin lumana da taimakawa jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Yadda Mafarauci Ya Zakulo Katukan Zabe Na PVC a wani Dajin jihar Anambra Yan Kwanaki Kafin Zabe

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164