Yaro Dan Shekara 6 Ya Bindige Malamar Makaranta A Amurka
- Wani dalibi dan shekara 6 a wata makarantar firamare a jihar Virginia na Amurka ya bindige malamar makaranta
- Steve Drew, shugaban yan sanda na yankin ya tabbatar da afkuwar lamarin, yana mai cewa malamar tana asibiti har hannun Allah
- George Parker, shugaban makarantu na yankin da abin ya faru ya nuna bakin cikinsa da damuwa kan lamarin, ya yi kira ga al'umma su taimaka a dena bari matasa na samun bindiga
Virgina, Amurka - Wani yaro dan shekara shida ya bude wuta a aji a wani makarantar 'firamare' da ke jihar Virginia a ranar Juma'a inda ya yi wa malami mummunan rauni, a cewar yan sanda.
Babu wani dalibi da ya yi rauni sakamakon harbin da ya faru a Richneck Elementary School a birnin da ke kusa da teku, rahoton Aljazeera.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Harbin da dalibin ya yi ba kuskure bane - Yan sanda
Shugaban yan sanda na yankin mai suna Steve Drew, yayin taron manema labarai ya ce.
"Wanda ya yi harbin dalibi ne dan shekara shida. Yanzu haka yana hannun jami'an yan sanda.
"Ba kuma harbi ne na kuskure ba."
BBC ta rahoto dan sandan ya ce malamar da aka harba shekarunta sun kai 30 kuma ana ganin raunin na barazana ga ranta.
Shugaban makarantu na yankin, George Parker ya ce:
"Labarin ya kada ni, ina cikin bakin ciki.
"Muna bukatar hadin kan al'umma don ganin cewa matasa ba su mallakar bindigu."
Harbe-harbe a makarantu matsala ce da ke adabar Amurka, a baya-bayan nan wani dan bindiga dan shekara 18 ya kashe yara 19 da malamai biyu a Uvalde, Texas.
An kiyasta cewa mutane kimanin 40,000 ne suka rasu a Amurka a bara sakamakon harbin bindiga, wasunsu hatsari wasu kuma yunkurin kare kai, tsautsayi da sauransu.
Mai gida ya bindige matarsa da bindiga yana zaton babban dansa ne da ke barazanar masa illa
A wani rahoton, yan sanda a jihar Bauchi sun kama wani magidanci dan shekara 40 mai suna Nuhu Umar Usman kan zarginsa da halaka matarsa, Ladi Usman.
Mai magana da yawun yan sandan Bauchi, SP Ahmed Wakili, ya sanar da hakan a ranar Juma'a, ya kuma ce an kai wacce abin da ya faru da ita asibiti, likita ya tabbatar ta cika.
Asali: Legit.ng