Matashin da Yayi Watsi da Karatun Likitanci, Yana Samun N265m Kowanne Wata a Sana'ar Haya
- Wani matashi mai shekaru 30 ya bayyana yadda ya fara neman kudi ta hanyar bada hayar dakuna bayan ya sanyasu a wata shafin yanar gizo
- Chris Choi ya ce dabarar kasuwancin tazo masa ne yayin da ya ziyarci kudancin Korea kuma ya zauna a Airbnb
- Ya fara amfani da kudin da yake tarawa ne sannan ya ari wasu daga abokinsa don fara kasuwancin, wanda a yanzu yana samun kimanin $600 duk wata
Chris Choi ya bayyana yadda yake shirin zuwa makarantar likitancin hakora kafin ya ziyarci kudancin Korea da ganin irin kasuwancin da abokansa suke.
Yaso kafa tsayayyen kasuwanci yayin da yake zuwa makaranta. Chris Choi ya ce yana samun kimanin $600 duk wata ta hanyar bada hayar dakuna.
Zuwansa Korea shine tushen kasuwancinsa
Yayin da ya kai ziyara ga abokansa a kudancin Korea, ya tsaya a wani Airbnb (dakin saukar baki) inda yayi mamakin gane yadda mai masaukinsa ya mallaki dakin saukar baki da dama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Choi, wanda ya bashi masaukin ya fada masa yana amfani da wani tsarin bada haya inda yake tallata kadarorin.
Daga lokacin ne dabarar tazo masa. Yayi bincike tare da gano akwai karancin dakunan saukar baki a wurarensa sannan ana amsar $150 zuwa $250 duk kwana daya kuma suma otel a yankin suna amsar kudi daya.
Ya gwada kudin hayar wata tare da cewa, idan ya bada hayar daki kan $180 kwana daya, a cikin kwanaki goma kacal cikin wata daya, sauran kwanakin zasu zama ribarsa.
Bashi da jarin farawa
Matsalar daya ce, bashi da isashshen kudi a lokacin. Ya kirga ya ga zai kashe $8,000 kafin ya fara
Kamar yadda ya bayyana, kudin shine na hayan wata dayan farko, tari da kuma kayan dakin.
Ya kara da bayyana yadda ya ari kudi tare da hadawa da kudin da yake tari na makarantar likitancin hakora don fara kasuwancin.
A watanni takwas da farawa, Choi ya ce abubuwa sun tafi lafiya lau, sai dai ya sami wasika daga ofishin da suka bashi haya na cewa ya karya dokoki da yarjejeniya ta hanyar dora sunayen kadarorinsu da Airbnb.
Sun yi masa barazana idan bai daina ba, za su daureshi. Bayan barazanar da ya samu, ya bukaci samun wani wurin , inda ya dace da wasu masu gidan hayar iyali daya, saboda suna rubuta kwantirakinsu.
Cikin sa'a ya dace ya gamsar dasu game da kasuwancinsa, wanda a yanzu yana samun kimanin $12,000 duk wata. Bayan 'yan bukatu, yana samun ribar ta ko ina daga $5,000 zuwa $8,000 a matsayin riba.
Sai daga bisani ya fahimci zai iya samu tare da dora sauran kadarorin a Airbnb.
Choi ya dakatar da burinsa na zama likitan hakora
Saboda ganin irin kudaden da yake samu, ya yanke shawarar dakatar da burinsa na zuwa makarantar likitancin hakora na wucin-gadi don mayar da hankali a kasuwancinsa.
Amma bai sanar da iyayensa ba, ya dai cewa makarantar zai jinkirta karatunsa zuwa zango na gaba don kasuwancinsa.
Choi ya ce, a yanzu yana kula da kadarori sama da 100 duk daga sashi mai tsada da manyan gidaje.
Ya ce yana shirye-shiryen bada hayar manyan gidaje maimakon kananan dakuna.
Haka zalika, ya bayyana yadda ya kulla alaka mai karfi da masu bada hayar. A yanzu yana samun $600,000 duk wata, wanda kwangilolin zasu kai $10 miliyan a karshen 2022.
Asali: Legit.ng