Alhakin kisan Jamal Khashoggi ya rataya a wuyana, in ji Yariman Saudiyya

Alhakin kisan Jamal Khashoggi ya rataya a wuyana, in ji Yariman Saudiyya

- Yariman Saudi, Mohammed Salman ya ce alhakin kisan Khashoggi ya rataya wuyansa ne saboda karkashin mulkinsa aka yi

- Yariman ya sanar da hakan ne a hirar da aka yi da shi wacce za a gabatar a mako mai zuwa

- Majalisar dinkin duniya dai ta ce a binciki Yariman Saudi da kuma sauran manyan jami'an kasar akan kisan

Yariman kasar Saudi Arabia ya ce alhakin kisan dan jarida Jamal Khashoggi da aka yi yana wuyansa domin abin ya faru ne karkashin mulkinsa kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Basaraken, Mohammed bin Salman, har yau dai bai fito ya yi bayani ga jama'a ba akan kisan dan jaridar da aka yi a ofishin jakadancin Saudi da ke Istanbul.

CIA da wasu jami'an gwamnatin gamma sun ce shi ya bada umarni amma jami'an Saudi sun ce babu hannunsa.

Kisan ya jawo cece-kuce a fadin duniya inda kimar yariman ta ragu hakazalika ta zama kalubale ga shirin kasar na yalwata tattalin arzikinta zuwa kasashe manya masu siyarda man fetur a duniya.

Tun daga nan yariman bai kara ziyartar Turai ko Amurka ba.

DUBA WANNAN: Sabbin kirkire-kirkire ne hanyar inganta aikin gwamnati, in ji Yemi-Esan

"Ya faru a karkashin mulkina. Ni ke da laifin saboda ya faru a karkashina," ya sanar da Martin Smith, a hirar da suka yi wacce zata fito sati mai zuwa.

"Yariman Saudi Arabia," zai yi magana a ranar 1 ga watan Oktoba wacce tayi daidai da shekara daya da kisan Khashoggi.

Bayan musantawa da suka yi da farko, jami'an Saudi sun dora laifi akan bata garin jami'ai.

Saud al-Qahtani, tsohon mai bada shawara a masarautar shi ya baiwa makasan bayani akan aiyukan Khashoggi kafin su aikata aika-aikar, in ji jami'in da ya gabatar da karar a kotu.

Da Smith ya tambayi yariman ta yadda aka yi kisan ba tare da ya sani ba, yariman ya ce: "Muna da mutanen miliyan 20 a kasar nan. Akwai kuma ma'aikatan gwamnati miliyan 3."

Wani babban jami'in gwamnatin Amurka ya ce a watan Yuni gwamnatin Trump ta dinga takura Riyadh akan bayanan wadanda suka aikata mummunan aikin.

Mutane 11 daga Saudi aka gurfanar gaban kotu da kisan amma zaman kotun da aka yi ba yawa.

Wani rahoto na majalisar dinkin duniya ta bukaci a binciki yariman Saudi da sauran manyan jami'an kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng